Mutum 4 sun mutu a turmutsutsun karɓar sadakar azumi a Katsina

[ad_1]



Aƙalla mutum huɗu ne suka rasa rayukansu a wani turmutsutsu da ya faru yayin rabon sadakar azumin Ramadan a unguwar  Kofar-Guga da ke cikin ƙwaryar birnin Katsina.

Da yake bayar da tabbaci, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Aliyu Abubakar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ƙwarai.

Ya ce turmutsutsun ya faru ne a da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar 26 ga Fabrairu, 2026, bayan da aka samu taruwar jama’a masu yawa a gidan wani attajiri da ke raba sadaka a yankin.

A cewarsa, bayan samun kiran gaggawa a ofishin ’yan sanda na Central Police Station, jami’ai sun garzaya wurin domin kai ɗauki.

Ya kuma ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin ba su kulawar gaggawa, sai dai mutum huɗu daga cikinsu daga bisani suka rasu sakamakon munanan raunukan da suka samu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bello Shehu, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Ya kuma bayar da umarnin fara cikakken bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Haka kuma, rundunar ta shawarci duk masu niyyar raba sadaka ga jama’a da su sanar da ’yan sanda tun da wuri, domin a tanadi isasshen tsaro da kula da tsari, don kare rayuka da dukiyoyi da kuma gujewa sake afkuwar makamancin haka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *