Tsakanin ‘Yan Mata Da Samari Su Wa Suka Fi Karya A Soyayya?
Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi soyayya, duba da yadda ake samun kalubale a wasu wuraren game da soyayya. Shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko Tsakanin Mata da Maza wa ya fi karyar soyayya a yanzu?, Shin me yake janyo hakan?, Ta wacce hanya za a bi domin magance matsalar?”.
- An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce
- Jam’iyyar NNPP Za Ta Yi Gagarumin Tasiri A Zaben 2027 – Kwankwaso
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
karya suke karewa har ya tsofe ko ta tsofe ba a ankara ba zuciya ta ginu da yaudarar da karyar soyayya.
Sunana Hafsat Sa’eed, daga Naija:
Gaskiya maza sun fi mata karya, amma dai kowanne yana kwatantawa. Maza nasu ya fi karfi sakamakon ba sa soyayyar gaskiya sai ta kudi. Mafi yawanci idan mutum ya ga yana da kudi haka zai ta yaudarar mace, su nemi wannan su nemi waccen, suna daga mata hankali, tun da an riga da an saka rayuwar karya a yanzu. Wani ma baka son shi, saboda kudin shi za ka ga kana bibiyar shi, ka yi ta nuna masa so da kalaman karya. Saboda abin hanun shi, a wasu bangaren maza haka za ki ga, saboda suna da kudin, yayin da suka yi ‘dumping’ din wannan, za su dauko waccen, duk dan suna ganin suna da kudi, su kuma matan su yi ta bin su.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:
A ra’ayina dangane da darasin da ake tattaunawa a wannan mako. Mata ne suka fi karya a soyayya. Saboda suna son nuna kansu a matsayin na musamman, wato abin da ake kira ‘packaging’ da turanci. Saboda yadda wasu matan ke nuna matsuwa da yin aure, suna nuna kyawawan abubuwan da za su jawo hankalin namiji ko duk wanda suka ɗana tarko suna son su aure shi, ta yadda zai gamsu lallai sun dace da zaman aure. Ba ina nufin maza ba sa karyar arziki da sauran halaye irin na rashin gaskiya a wajen wadanda suke so ba, amma dai mata sun fi son a dauke su da kima da martaba, ko da kuwa a zahiri ba hakan suke ba. Babbar hanyar da za a bi a kaucewa yawan karya a soyayya ko lokacin neman aure shi ne, a ji tsoron Allah, a kiyaye ka’idojin da addinin musulunci ya gindaya ga masu neman aure. A guji yin abin da za a yi daga baya a ji kunya, a kyautata zato, a kuma tsare gaskiya don samun zuriya tagari.
Sunana Hassana Sulaiman, daga Hadejia Jihar Jigawa.:
Eh, a nawa mahangar matan mun fi karya a soyayya musamman cikin zamanin nan da ake sanya gasa ta karyar da kuma kece reni cikin abokai. Abin da nake ga shi ke janyo hakan bai wuce kowa na san burgewa ne na wanda ke tare da shi da kuma san a sani da cewa wane ya kai. Hanyar da nake ga idan an bi za a magance matsalar bata wuce koyon yin gaskiya a aikace ba, da kuma yayin furucin mu da duk wani motsin da muke na rayuwar soyayyar. Shawarar da ya kamata mu bawa junanmu a nan ita ce, mu daina sanya gasa da nuna halin kece-reni cikin mu’amalar mu da junan mu, da kuma daina sanyawa ranmu tare da daukar abin da ba za mu iya ba ,mu ce zamu iya dan a nuna mu cikin mutane.
Sunana Abubakar Usman, Malam Madori, A Jihar Jigawa:
Karya a soyayya bata takaita ga jinsi daya ba, maza da mata duka na iya aikatawa gwargwadon halinsu da manufarsu. A zamanin yau, ana ganin maza na yin karyar soyayya don biyan bukatar jiki, ya yin da mata ke yin hakan don samun amfani kamar kudi ko kulawa. Duk da haka, akwai masu gaskiya a duka bangarori. Domin magance wannan matsala, ya zama dole a gina soyayya bisa gaskiya, amana da fahimta. A guji yin gaggawa wajen fara soyayya, a yi nazari kan halayen juna, a kuma nemi shawarar iyaye ko amintattu. Zaben mutum mai tarbiyya da tsoron Allah yana taimakawa rage hadarin yaudara.
Sunana Fatima Nura Kila, Jihar Jigawa:
Kowanne suna tabawa ba ga mazan ba, ba ga matan ba. Abin sai godiya kawai, amma duk cikin mazan da matan ba na cirewa. Abin da yake janyo hakan shi ne, san abin duniya da kuma mutum ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba. Mu daina yi wa junanmu karya, domin a musulunce ma karya haramun ce, mu rinka saka gaskiya a lamarinmu. Yin karya a soyayya ba shi bane, mutum ya fadi komai nasa yadda yake ba karya a ciki, Hakan zai sa mutum ya samu Abin da yake so.
Sunana Khadija Auwal, Koki, A Jihar Kano:
A ganina kowane bangare suna yi, domin mutane sun mayar da karyar ba abakin komai ba. Abin da yake janyo hakan shi ne matan sun sa karya a cikin tafiyar, haka su ma mazan, domin kuwa suna ganin kamar sai an yi karya sannan auran zai tafi yadda ake so. Ta hanyar fadin gaskiya da kuma cikakken bincike kafin auran. Shawara ita ce idan har ana son juna da gaske kuma har ana son ayi aure to, a daina boye komai, wato dai a daina karya a fito da asalin gaskiya, domin zaman yayi yadda ake so.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Eh, to! gaskiya kowanne bangare suna yi, amma yanzu karya a soyayya maza sun fi gaskiya, wasu mazan za su zo kamar da gaskiya sai ka ga yaudara ce ta kawo su ba aure ba. Wasu mazan suna kafa huja da mace sun fi son makaryata shi ya sa suke zuwa da karya gun mace. To ‘yadda za’ a yi magance wa matsalar shi ne da namiji ya zo in dai aure yake nema to, ya turo iyaye shi ayi magana shi ne kawai. Shawarata shi ne ga masu irin wanan hali su ji tsoron Allah, saboda duk abin da ka yi wa wani sai an yi mashi Allah baya bacci Allah ya bamu dacewa.