Bayern Munich na shirin tsawaita kwantaragin Harry Kane

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta fara tattaunawa da Harry Kane na Ingila kan shirin tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zamanshi a ƙungiyar ta Jamus.

A watan Agustan 2023 ne kyaftin ɗin na Ingila mai shekaru 32 ya koma Bayern Munich daga Tottenham a kwantiragin shekaru 4 kan farashin yuro miliyan 100 ko kuma fam miliyan 86 da dubu 400.

Daga komawar shi ƙungiyar kawo yanzu Kane ya zuwa ƙwallaye 119 yayin da ya taimaka aka zura wasu 30 a wasanni 126 baya ga lashe kofin Bundesliga na kakar wasan 2024/2025 — kofi na farko da tauraron na Ingila ya ɗagawa a rayuwarsa ta ƙwallo.

Da yake magana a yayin taron Bundesliga da aka gudanar a Frankfurt, Daraktan wasanni na Bayern Munich, Max Eberl, ya bayyana cewa ƙungiyar na tattaunawa da Harry Kane cike da fatan tsawaita kwantiraginsa.

A cewar Max Eberl sanin kowa ne, Bayern Munich na buƙatar ci gaba da aiki da Kane duk da cewa tsohuwar ƙungiyarsa, Tottenham da ma wasu ƙungiyoyi a Firimiyar Ingila na zawarcin komawarsa gida.

Sai dai ko a watan Oktoban bara, Kane ya bayyana cewa ko shakka babu zai ci gaba da zama a Bayern yayin da ya ce ya ajiye batun komawarsa Firimiyar Ingila zuwa wani lokaci a nan gaba.

A kakar da ta gabata, Kane ya zura ƙwallaye 34 a wasanni 30 ciki har da 21 a wasannin Bundesliga 19 wanda ke nuna yiwuwar tauraron na Ingila ya iya goge tarihin Robert Lewandowski da ya zura ƙwallaye 41 a kaka guda ƙarƙashin gasar ta Bundesliga.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *