Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu

[ad_1]



Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya.

Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito.

A watan Nuwambar nan ne labaran ƙanzan kurege suka riƙa yaɗuwa cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya.

Bayanai sun ce tun dai cikin watan Oktoban da ya gabata, aka kwantar da Dharmendra a asibitin Candy Hospital da ke birnin Mumbai gabanin sallamar shi ranar 12 ga watan nan, sai da kuma ya koma ga mahaliccinsa da safiyar yau Litinin.

Firaiministan Indiya, Narendra Modi ya bayyana alhininsa ga rashin jarumin wanda ya bayyana da “ƙarshen shekarun fina-finan Indiya.”

Dharmendra wanda ya haska a fina-finai fiye da 300, ya shafe aƙalla shekaru 60 a masana’antar Bollywood, kodayake an fi ganin shahararsa a fina finai irin Sholay da Phool Aur Patthar baya ga Satyakam da Chupke Chupke sai kuma Dharam Veer da Anupama.

BBC ya ruwaito cewa, Dharmendra ya fara fim ne tun zamanin fina-finai marasa launi, ma’ana tun zamanin hoton bidiyo fari da baƙi, inda a shekarar 1960,  ya fito a matsayin mataimakin jarumi, wato ‘supporting actor’ a fim ɗin Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere.

Dharmendra ya auri matarsa ta farko Parkash Kaur a shekarar 1954 suka kuma haifi ’ya’ya huɗu da suka ƙunshi Sunny Deol da Bobby Deol da Vijeta Deol sai kuma Ajeeta Deol.

A shekarar 1979 ne Dharmendra ya auri matarsa ta biyu kuma fitacciyar jaruma, Hema Malini inda suka haifi yara biyu da suka ƙunshi Esha Deol da Ahana Deol.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *