Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Katsina, ta ce dakarun sojin Najeriya sun kashe ’yan fashi bakwai a jihar.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu ne, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce sojojin sun kuma ƙwace babura huɗu a Karamar Hukumar Kankara.

Ya ce samamen ya ɗauki sama da awa biyu a ranar Alhamis, bayan samun bayanan sirri cewa ’yan fashin sun kai hari ƙauyen Baba.

Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wani hari da ’yan fashi suka kai  wani masallaci.

Harin ya yi sanadin salwantar rayukan sama da mutane 30, rahotanni kuma na cewa adadin ya kai kusan 50.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *