Hatsari: Mutum biyu sun mutu, 16 sun jikkata a Jos

[ad_1]



Mutane biyu sun rasu, wasu 16 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wata tankar mai da wasu motoci guda biyar a kusa da Polo roundabout a garin Jos, Jihar Filato.

Kakakin Hukumar Kiyaye Lafiyar Hanya (FRSC) a jihar, Peter Yakubu Longsan, ya ce a yammacin Lahadi abin ya faru kuma an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a cikin birnin Jos.

A cewarsa, “Mutane 18 ne hatsarin ya shafa, inda maza biyu suka mutu a wurin, sauran 16 kuma sun samu raunuka daban-daban. An kai su Asibitin Ƙwararru na Jihar Filato da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham (BUTH). An ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a BUTH.”

Shaidu sun ce burkin tirelar  ya tsinke ne, inda ta ƙwace bayan ta wuce Asibitin Kwararru na Jihar Filato, inda ta ci gaba da gangarawa har ta yi karo da motoci kafin ta tsaya.

Longsan ya ƙara da cewa, “Abin godiya, ba a samu zubewar man da yankin ya ɗauko ba, hakan ya rage haɗarin tashin gobara. Hukumomin da suka halarci wurin sun haɗa da FRSC, ’yan sanda, NSCDC, ’yan banga, sojoji, hukumar kashe gobara, VIO da kuma ’yan Red Cross.”

Shugaban FRSC na jihar, Olajide E. Mogaji, ya yaba da haɗin gwiwa da fahimtar juna da hukumomi da al’umma suka nuna wajen tabbatar da tsaron hanya.

Ya kuma yi kira ga masu amfani da hanya da su kasance masu taka-tsantsan musamman a wannan lokacin bukukuwa da ake yawan yin tafiye-tafiye.

Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne makonni biyu bayan wasu hatsarori makamancin haka da suka auku a kan titin Zaria da Jos-Bauchi, inda mutane 19 suka mutu ciki har da ɗaliban Jami’ar Jos.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *