An sake kai sabon hari Filato bayan ziyarar Tinubu
[ad_1]
Ƙasa da sa’o’i 24 bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da iyalan waɗanda aka kashe a harin Angwan Rukuba da ke Jos, an sake kai wani hari a Jihar Filato, wanda ya yi sanadin rasa rayuka.
Idan za a tuna, Tinubu ya gana da iyalan waɗanda harin ya shafa a Filin Jirgin Sama na Yakubu Gowon, inda ya jajanta musu.
Tinubu, ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki ƙwararan matakai domin tabbatar da cewa irin wannan ɗanyen aikin bai sake faruwa ba.
Sai dai, kalaman shugaban ba su yi tasiri ba, domin a daren ranar Juma’a, wasu ’yan bindiga sun ƙaddamar da hari a ƙauyen Nyango Gyel da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, inda aƙalla mutum uku suka riga mu gidan gaskiya.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyen ne da misalin karfe 10:40 na dare, inda suka rinƙa harbin mai kan-uwa-da-wabi kafin daga bisani suka tsere suka bar mutane cikin jimami.
Sakataren ƙungiyar matasan Berom, Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana harin a matsayin rashin imani.
Tengwong, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen gudanar da bincike domin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa, tare da daƙile duk wani hari a nan gaba.
Haka kuma, ya buƙaci mazauna yankunan karkara na Jos ta Kudu, Riyom, da Barkin Ladi da su ƙara sanya ido tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana.
Duk da ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Alfred Alabo, ya ci tura, domin ya ce yana cikin wani taro ne.
Amma ya yi alƙawarin yin ƙarin bayani daga baya.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani martani daga wajensa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link