Ronaldo Ba Shi Da Ikon Yanke Hukunci A Gasar Saudi Pro League – Mahukunta
[ad_1]
Mahukuntan gasar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya (Saudi Pro League) sun ƙaryata raɗe-raɗin da ke cewa Cristiano Ronaldo na da tasiri wajen yanke manyan hukunci a gasar. Sun jaddada cewa babu wani ɗan wasa ko yana buga gasar ko a’a da ke da ikon tsara manufofin gasar ko na kowace ƙungiya.
Wannan martani ya biyo bayan jita-jitar da ta karaɗe kan makomar Ronaldo a Al-Nassr, bayan rashin shiga jerin ’yan wasan da suka fafata da Al-Riyadh a wasan Litinin. Rahotanni daga Portugal sun yi iƙirarin cewa ɗan wasan mai shekaru 41 ya ƙi buga wasan ne sakamakon tangarɗar alaƙa tsakaninsa da shugabannin ƙungiyar.
- Ronaldo Zai Iya Buga Wasan Farko Na Kofin Duniya Bayan Hukuncin FIFA
- Nijeriya Da Saudiyya Sun Ƙara Ƙarfafa Alaƙa Kan Inganta Harkokin Hajji Da Umrah
Duk da wallafa hotunan atisaye tare da abokan wasansa kafin wasan, Ronaldo bai bayyana a filin wasa ba, lamarin da ya ƙara haifar da tambayoyi kan ko zai buga wasan da Al-Nassr za ta yi da Al-Ittihad ranar Juma’a.
BBC Sport ta ruwaito cewa dangantaka tsakanin Ronaldo da Al-Nassr ta ƙara tsami ne bayan tsohon abokin wasansa na Real Madrid, Karim Benzema, ya koma Al-Hilal daga Al-Ittihad. Benzema ya fara rayuwa a sabuwar ƙungiyarsa da zura ƙwallaye uku a wasansa na farko, abin da ya ƙara jan hankali a gasar.
[ad_2]
Source link