Wannan Wasika Ta Bayyana Kaunar Dake Tsakanin Sin Da Afirka
A kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu tsoffin sojojin kasar Zimbabwe, wadanda suka taba halartar gwagwarmayar neman ’yancin kan kasar, suka rubuta masa, inda shugaban ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, “Kasar Sin a ko da yaushe ita ce kawar kasashen Afirka, wadda ta samar da taimako ga yunkurin ’yantar da al’ummun Afirka, kuma tana kokarin hadin gwiwa da bangaren Afirka wajen neman ci gaban tattalin arziki da zamanantarwa.” Wannan magana, a ganina, ta nuna ma’anar huldar dake tsakanin Sin da Afirka.
Bayan da aka kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, kasar ta samar da taimako ga al’ummun kasashen Afirka bisa yunkurinsu na neman ’yancin kan kasa, inda dimbin ’yan gwagwarmaya na Zimbabwe suka samu horo daga kasar Sin, lamarin da ya zama abun da ya cancanci tunawa a tarihin huldar kasashen Sin da Zimbabwe. A zahiri, ya kamata a yi kokarin gadon wannan hulda mai cike da kauna, ta yadda za mu iya amfani da ita wajen dakile yunkurin wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma na samar da bahaguwar fahimta da neman lalata hulda a tsakanin al’ummun Sin da Afirka.
Sai dai zuwa yanzu, wani abu mai kyau da muka samu shi ne, muna iya ganin yadda huldar dake tsakanin Sin da Afirka ke ta kara karfi, bisa cudanyar mutane, da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da ake yi tsakaninsu. Misali, Issah Abiola, direba mace mai tuka jirgin kasa ta farko ta kasar Najeriya. Bayan da ta zama ma’aikaciyar wani kamfanin kasar Sin, ta samu damar koyon fasahar tuka jirgin kasa, har ma ta zama daya daga cikin direbobi masu tuka karamin jirgin kasa na birnin Abuja. Sa’an nan a nasa bangare, He Jie, wani dan wasan gudun dogon zango na kasar Sin, bayan da ya ga yadda mutanen kasar Kenya ke matukar kaunar wasan tsere na dogon zango, wannan batu ya burge shi sosai. Daga bisani, ya tafi kasar Kenya don neman samun horo sau da dama cikin shekaru 3 a jere, inda ya yi kokarin kyautata fasaharsa ta gudu, ta hanyar samun horo tare da dimbin fitattun ’yan wasa na kasashen Afirka. Zuwa yanzu, ya riga ya zama mai rike bajintar maza a wasan gudun Marathon ta kasar Sin.
Ta wadannan misalai za mu iya ganin cewa, cudanyar da ake yi tsakanin mutanen kasar Sin da na kasashen Afirka tana haifar da ci gaban daidaikun mutane, da damar karfafa fahimtar juna, da amincewa da juna, da kauna, a tsakanin bangarorin Sin da Afirka.
Sa’an nan, a cikin wasikar da ya rubuta, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce shekarar 2026 ita ce shekarar “cudanyar mutane da musayar al’adu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka”. Wannan take ne na jerin ayyukan cudanya da aka tabbatar da su a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 2024, kuma yanzu ana aiwatar da ayyukan bisa shiri. An ce, za a gudanar da bukukuwa da yawansu ya kusan kai 600 a fannonin aikin ilimi, da al’adu, da yawon shakatawa, da dab’i, da wasannin motsa jiki, da dai sauransu, bisa hadin gwiwar bangarorin Sin da Afirka, inda za a samar da dandalin cudanya ga jama’ar bangarorin biyu, da damar kara kyautata hulda a tsakaninsu.
Ta wadannan bukukuwa, ake neman kula da ayyukan fannoni guda uku, wato ci gaban matasa, da rage talauci, gami da kimiyya da fasaha, ta yadda za a karfafa kauna da hadin kan al’ummun Sin da Afirka. Kana ta hanyar kokarin gadon kaunar da ta kasance tsakanin Sin da Afirka, dukkanmu za mu samar da gudunmowa ga yunkurin bangarorin Sin da Afirka na hadin gwiwa da juna a kokarin zamanantar da kansu. (Bello Wang)