Shin Michael Carrick Ya Gyara Manchester United Ne?
[ad_1]
Za a iya cewa an bude sabon shafi a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tun bayan korar mai koyarwa Ruben Amorim, bayan ya shafe watanni 14 yana koyar da kungiyar ta kasar Ingila.
Tun bayan nada Machael Carrick kociyan kungiyar na rikon kwarya abubuwa da dama suka canja musamman samun nasara a wasanni biyu a jere, kuma nasarar ta ban mamaki, domin manyan kungiyoyin Ingila, Manchester City da Arsenal ya doke, wadanda su ne a matsayi na daya da na biyu a halin yanzu a gasar Premier ta Ingila.
- CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki
- Gobara Ta Hallaka Mutum 2, Ta Lalata Dukiya Ta Biliyan 1.59 A Bauchi
Michael Carrick yana da kwarewar da ba za ta sa ya shagaltu ba kan cewa ko yana son zama kocin Manchester United na dindin, sai dai yana cike da farin ciki lokacin da ya bayyana cewa ‘yayansa sun halarci wasan kungiyarsa da Arsenal a filin wasa na Fly Emirates ranar Lahadi, inda suka shiga sahun dubban magoya baya da suka barke da murna lokacin da
Matheus Cunha ya ci kwallon da ya bai wa United nasara da ci 3-2, kuma nasararsu ta farko kenan a gidan Arsenal cikin shekara takwas.
Sannan an nuno mai karamin hannun jari a Manchester United Sir Jim Ratcliffe cikin annashuwa lokacin da aka haska shi a Emirates. Babu lokuta da dama na yin murmushi sama da shekara biyu da ya sayi hannun jari a kungiyar ganin irin rashin katabus da suke yi.
Michael Carrick ya samu nasarar lashe wasanninsa na biyu tun fara jagoranci a United. Wani abu da Ruben Amorim ya taba samu sau daya cikin watanni 14 da ya yi a kungiyar – lokacin da ya samu nasarar wasanni uku a jere a farkon fara wannan kaka, abin da ya sa ya samu kyautar kocin da a fi kwazo na watan Oktoba.
Manchester United ta samu maki shida karkashin Carrick. Amorim kuwa ya shafe wasanni biyar kafin ya samu haka – inda daga nan ya yi rashin nasara a wasanni uku da suka bi baya.
Makonni shida da suka wuce, babu wanda zai zabi Carrick a matsayin kocin United na gaba a kan kocin Crystal Palace, Oliber Glasner. Amma yanzu akwai muryoyi da dama da suka gargadi United kan maimaita abin da ya faru a kakar wasa ta 2018 zuwa 2019.
Idan mai karatu bai manta ba, kakar wasanni bakwai da suka wuce, aka nada Ole Gunnar Solksjaer a matsayin kocin riko, ya lashe wasanni takwas a jere, sai kuma wasanni shida cikin tara da suka bi baya ya samu gagarumar nasara a hannun Paris sT-Germain a gasar Zakarun Turai, lokacin da United ta farfado daga kwallo biyu da PSG ta Parc des Princes – daga nan aka ba shi aikin kocin kungiyar na dindindin.
Solskjaer ya jagoranci Man United zuwa wasan karshe na gasar Europa a 2021, inda Billareal ta doke ta a bugun fenariti. Amma kuma samun nasarar wasanni na iya juyawa cikin gaggawa kamar yadda ra’ayoyi suka bayyana – duk da cewa Carrick bai nuna alamun za a ci United da sauki ba a yanzu.
Sai dai Carrick ya kawo sauyi na wasu matsaloli da aka samu lokacin Amorim – inda ya koma amfani da tsarin saka ‘yan wasa na 3-4-3 zuwa ‘yan wasa hudu a baya, da dawo da Kobbie Mainoo cikin tawagar da kuma mayar da kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes komawa buga wasa can kusa da gaba, ba kamar lokacin Amorim ba.
Ya kuma wasu sauye-sauye masu karfi. Matakin da ya dauka na fara wasa da Patrick Dorgu a bangaren hagu na gaban Man United maimakon Matheus Cunha ya fara yin tasiri. Dorgu ya ci kwallo biyu a wasanni biyu karkashin Carrick, inda shi ma Cunha ya shiga fili ya ci wa United kwallo mai kyau da ta bai wa kungiyar nasara kan Arsenal da kuma bayar da kwallo a ci a wasansu da Manchester City.
Sai dai, duk da irin wannan namijin kokari da Michael Carrick ya fara da shi, tsoffin ‘yan wasan kungiyar Roy Keane da Gary Nebille, ba su amince cewa a ba shi aikin kocin kungiyar na dindindin ba. Makonni uku da suka wuce, Carrick yana can yana hutunsa tare da Wayne Rooney a tsibirin Barbados.
A ranar Juma’a, sun zauna tare a Old Trafford don kallon yadda Kai Rooney ya taimaka wa tawagar ‘yan kasa da shekara 18 na Man United zuwa zagayen 16 na FA Cup – ajin matasa.
Sai dai yanzu ana ganin shugabannin kungiyar za su fara tunanin ba wa tsohon dan wasan nasu aikin na dindindin musamman idan ya cikawa kungiyar burinta na zuwa kofin Zakarun Turai.
Manchester United kawo yanzu tana mataki na hudu a kan teburin gasar ta Ingila, maki 8 tsakaninta da kungiyoyin Manchester City da Aston Billa, wadanda suke mataki na biyu da na uku. Sannan akwai tazarar maki 12 tsakanin Manchester United da Arsenal, wadda take mataki na daya a gasar ta Ingila, ya yin da ya rage saura wasanni 15 a kamala kakar wasa ta bana.
Tun da farko shugabannin kungiyar sun bayyana cewa za su bawa Carrick rikon kwarya zuwa karshen kakar wasa ta bana, domin hakan zai basu damar nutsuwa su tattauna sannan su zabi mai koyarwar da za su dauka domin bashi ragamar koyar da kungiyar na dindindin, kamar dai yadda aka bawa Ruud Bannistlerooy koyar da kungiyar a baya kafin daukar Ruben Amorim.
Wasu daga cikin masu koyarwar da ake danganta kungiyar da su sun hada da Oliber Glasner, wanda zai bar kungiyar Crystal Palace a karshen kakar wasa ta bana, sai kuma Eddie Howe, kociyan kungiyar Newcastle United.
Akwai kuma kociyan tawagar Brazil, Carlo Ancelotti, da Thomas Tuchel, wanda yake koyar da tawagar ‘yanwasan Ingila, da kuma Mauricio Pochettino, wanda a yanzu yake koyar da tawagar ‘yanwasan kasar Amurka. Shima kociyan tawagar jamus, Nagelsman, yana cikin masu koyarwar da ake dangantawa da aikin koyar da Manchester United a kakar wasa mai zuwa.
Idan har Michael Carrick ya yi kokarin ganin kungiyar ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa tabbas zai cika jerin wadanda za a kalla wajen ba wa babban aikin.
[ad_2]
Source link