Ramadan: ’Yan sanda sun tsawaita dokar zirga-zirgar ababen hawa a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sanar da tsawaita zirga-zirgar babura daga 7 na yamma zuwa 11 na dare har zuwa ƙarshen watan Ramadan.

A cewar kakakin rundunar, Buhari Abdullahi, an dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan tsaro domin bai wa al’umma damar gudanar da ibada da sauran harkokinsu a watan azumi cikin sauƙi.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Umar Ahmed Chuso, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu, tare da ɗaukar duk matakan tsaro da suka dace.

Ya kuma baza jami’an tsaro a wuraren ibada, manyan hanyoyi da wuraren taruwar jama’a domin tabbatar da zaman lafiya.

Rundunar ta shawarci masu babura da su bi dokokin hanya, su guji tuƙin ganganci, su yi rijistar baburansu, sannan suke yawo takardunsu a kowane lokaci.

Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.

A ƙarshe, rundunar ta gode wa shugabannin addini da ɗaukacin al’umma bisa haɗin kai da goyon bayan da suke ba su wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *