Har abada ba za mu taba jituwa da Tinubu ba — El-Rufai

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai taba yin abota ko hulxar siyasa ta kai tsaye da Shugaban Kasa Bola Tinubu ba, yana mai cewa hanyoyinsu ba su tava haduwa ba.

El-Rufai, wanda yanzu jagora ne a Jam’iyyar ADC, ya yi wannan bayani ne a wata hira da aka yi da shi a Trust TV. Ya ce akwai kuskuren fahimta da ake yi cewa shi da Tinubu abokai ne ko kuma abokan siyasa.

“Ina ganin ya zama dole a fayyace wannan. Akwai tunanin cewa na taba zama abokin Tinubu. Ba haka ba ne. Ba mu taba jituwa da Tinubu ba. Ba mu taba yin huldar kashin kai ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa goyon bayansa ga takarar Tinubu a 2023 ba saboda abota ba ne, sai dai ka’ida da biyayya ga tsarin jam’iyyar APC.

El-Rufai ya ce wasu jagororin addini daga yankin Kudu maso Yamma ne suka roke shi da ya tallafa wa fitowar dan takara Musulmi daga yankin.

Ya kara da cewa tun da APC ta kafa tsarin cewa bayan mulkin shekaru takwas na Muhammadu Buhari, mulki zai koma Kudu, ya ga wajibi ya tsaya kan wannan ka’ida.

“Ni daya ne daga cikin masu kafa APC ne. Mun yi yarjejeniya da Kudu, musamman Kudu maso Yamma, cewa bayan shekaru takwas na Buhari, mulki zai koma Kudu. Ka’ida ce, ba wai Tinubu ba,” in ji shi.

El-Rufai ya ce bayan da Tinubu ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar, ya yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar APC a zabe.

“Ka’idata ita ce na yi wa dan takarar jam’iyyata aiki a kowanne zabe, ko ina son shi ko ba na son shi. Tinubu ya fito, sai na ba yi dukkan kokarina don ya yi nasara. Kuma hakan na yi,” in ji shi.

Sai dai ya ce bambance-bambancen ra’ayi da falsafar mulki ne suka sa shi da Tinubu ba su taba samun daidaito ba.

“Ba mu taba yin fada ba. Amma ba mu taba samun wurin da za mu yi daidaito ba. Ba mu taba jituwa ba,” in ji shi.

El-Rufai ya caccaki tsarin mulkin Tinubu

Nasir El-Rufai, ya yi suka kan abin da ya kira kamun ludayin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ba ta dace da fahimtarsa ta hidimar jama’a ba.

“Ina cikin gwamnati ne don aiki, don sakamako da ingantaccen aiki. Hidimar jama’a ba ta da alaka da tara kudi don kanka. Ba ta da alaka da satar dukiya. Ba ta da alaka da nada abokanka ko ’yan uwanka,” in ji shi.

Ya kara da cewa ko da a ce an tabbatar da nadinsa a matsayin minista a gwamnatin Tinubu, ba zai dade ba.

“Ko da tayin da Tinubu ya yi min na zama minista ya tabbata, da na bar gwamnati tun da dadewa. Kamun ludayin wannan gwamnati ta saba da duk abin da aka koya min a matsayin Musulmi, dan Arewa, da kuma dan Najeriya,” in ji El-RUfai.

Ya ce bambancin ra’ayi da dabi’u tsakanin shi da Shugaban kasa ya sa ba zai yiwu su yi aiki tare na dogon lokaci ba.

“Wadannan mutane ba don mulki suka zo ba. Don tara kudi suka zo, kawai. Mu mutane ne daban. Saboda haka bai kamata ya zama abin mamaki ga wanda ya san ni da Tinubu ba, ganin cewa mu layi ne biyu da ba za su taɓa haɗuwa ba,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *