Sanatan Kwara Ta Arewa Umar Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamna
[ad_1]
Sanatan da ke wakiltar Kwara Ta Arewa, Sadiq Umar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kwara a 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Ilorin, wanda ya samu halartar shugabannin jam’iyya, matasa, mata da wakilan al’umma daga sassa daban-daban na jihar.
- Komawar Kwankwaso ADC, Zai Jawo Hankalin Manyan ‘Yan Siyasa Zuwa Jam’iyyar
- Kotu Ta Ɗage Sauraron Neman Beli Na El-Rufai Zuwa Gobe Laraba
Umar ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne domin ci gaban jihar, ba don buƙatar ƙashin kansa ba.
Ya yaba wa gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, bisa ƙoƙarinsa wajen inganta ababen more rayuwa.
Haka kuma, ya gabatar da shirye-shiryensa da suka haɗa da inganta wutar lantarki, tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da bunƙasa tattalin arziƙi ta fannoni kamar noma, haƙar ma’adanai, yawon buɗe ido da ƙananan sana’o’i.
Tsohon Kwamishinan jihar, Abdulmumin Katibi, ya ce wannan mataki yana da muhimmanci ga ci gaban jihar, yana mai cewa Umar ya riga ya bayar da gudunmawa mai tarin yawa a faɗin jihar.
[ad_2]
Source link