Lee Jae-Myung: Tabbas Za A Kyautata Hulda Tsakanin Koriya Ta Kudu Da Sin

[ad_1]

Kafin ya fara ziyara a kasar Sin a gobe Lahadi, shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Jae-myung, ya zanta da wata wakiliyar kafar CMG, inda ya bayyana imaninsa da huldar dake tsakanin kasarsa da kasar ta Sin, wadda ya ce za ta daga zuwa wani sabon matsayi, bisa tushen ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai Koriya ta Kudu a bara, gami da ziyarar da shi ma zai gudanar a kasar Sin a wannan karo.

Yayin da ya tabo batu kan ziyarar da ya gudanar a kasar Sin a lokutan baya, Lee Jae-myung ya ce, a duk lokacin da ya shiga kasar Sin, ya kan ji tamkar ya shiga wata sabuwar duniya, saboda manyan sauye-sauye da ci gaba da kasar Sin ke samu. A cewarsa, kasar Sin ta karkata ga raya bangaren makamashi masu sabuntawa cikin sauri, tare da samun babban sakamako, inda kasar ta zama kan gaba a duniya a wannan bangare, musamman ma a fannin hada na’urorin samar da lantarki ta hasken rana. Wannan batu, a cewar Lee, ya shaida kwarewar kasar Sin a fannin mayar da kalubale zuwa dama, da dora karfin kasa wajen kirkiro sabbin fasahohi, da jagorantar ci gaban masana’antu.

Sa’an nan, a lokacin da ya ambaci cudanyar da ya yi da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, Lee Jae-myung ya ce, shugaba Xi wani fitaccen shugaba ne mai hangen nesa, wanda za a iya hadin gwiwa, gami da kulla huldar taimakon juna da shi. A ganin Lee, ya kamata kasashen Sin da Koriya ta Kudu su yi kokarin neman bangarorin da za su iya rika hadin gwiwa da juna, don tabbatar da moriyar dukkan kasashen biyu, tare da kulla huldar amincewa da juna, da hadin kai, gami da cude-ni-in-cude-ka. Shugaba Lee ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping ya fahimci wannan bukata sosai, kana shi da kansa yana da imani da cewa, za a iya mayar da bukatar ta zama sakamako na gaske.

Ban da haka, Lee Jae-myung ya jaddada cewa, dangane da batun Taiwan, wanda kasar Sin ke dora matukar muhimmanci a kai, kasar Koriya ta Kudu za ta ci gaba da girmama manufar nan ta Sin daya tak a duniya, daidai da yadda kasar ke tsaye kan wannan matsayi a baya. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *