Amurka ta tuhumi Shugaban Venezuela da matarsa kan safarar miyagun ƙwayoyi
[ad_1]
Amurka ta tuhumi Shugaban Ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro, da matarsa, Cilia Flores, da manyan laifuka da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi.
Babbar Lauyar Ƙasar Amurka, Pamela Bondi, ta sanar da cewa an gurfanar da su a kotun Kudancin Gundumar of New York, bisa waɗannan tuhume-tuhume.
A baya, Amurka ta kai hare-haren sama a Venezuela, inda sojojinta suka kama Shugaba Maduro tare da matarsa a wani samamen soji da suka kai.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce an gudanar da wannan aiki ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron cikin gida na Amurka.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, Bondi ta ce ana zargin su da shiga harkar safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa da kuma laifukan safarar makamai.
Ta ce ana tuhumar Maduro da haɗa baki wajen aikata ta’addanci, shirya shiga da hodar iblis zuwa Amurka, mallakar manyan bindigogi da makamai masu hatsari domin kai wa Amurka hari.
Bondi ta ƙara da cewa za a yi musu shari’a a Amurka, inda za su fuskanci hukunci a gaban kotunan Amurka.
“Ba da jimawa ba za su fuskanci hukunci a ƙasar Amurka,” in ji ta.
Ta kuma yaba wa Shugaba Trump bisa amincewa da aikin da ya kai ga kama su, tare da gode wa sojojin Amurka bisa nasarar da suka samu.
Amurka ta jima tana zargin Maduro da jagorantar wata babbar ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ta duniya, zargin da ya sha musantawa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link