Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe

[ad_1]



Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe, mai wakiltar Nafada ta Kudu, Adamu A. Musa, ya zargi gwamnati da ‘yan majalisun jihar da kasa aiwatar da dokokin da suke zartarwa.

Ya ce akwai dokar da aka zartar shekaru takwas da suka gabata domin yaƙi da fyaɗe da cin zarafin mata da yara, amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba.

A cewarsa, majalisa tana yin doka sannan ta tura wa gwamna ya sanya hannu, amma daga baya a bar ta kamar ba ta da amfani.

Ya yi gargaɗin cewa irin wannan sakaci yana ƙara wa masu aikata laifi ƙwarin guiwa kuma yana haifar da ƙaruwar manyan laifuka.

Ya ce da ana aiwatar da dokokin, da tuni an rage irin waɗannan laifuka, amma a maimakon haka, idan aka kai rahoton laifi, masu kuɗi suna ɗaukar lauyoyi su fito da su ba tare da an hukunta su ba.

Ya kawo misalin wata ɗaliba a Kano da ake zargin shugaban makarantarsu ya kashe ta, inda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alƙawarin aiwatar da hukuncin kisa amma bai yi hakan ba har ya sauka daga mulki.

Haka kuma ya nuna cewa babu wani gwamna a jihohin Arewa da ya taɓa aiwatar da hukuncin kisa ga masu aikata irin waɗannan manyan laifuka.

Sai dai, ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin a fara aiwatar da dokokin a jihar nan gaba kaɗan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *