’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina

[ad_1]



’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata.

Shaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda suka kuma mamaye ƙauyen Bogga; ƙauyen Fulani da ke kan hanyar Kankia zuwa Ingawa.

Sakamakon haka, mazauna ƙauyukan Bogga, Taiba Badole, Arahiya Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo duk da ke yankunan Gachi da Fakuwa/Kafindangi, sun tsere daga gidajensu saboda tsoron hare-hare.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun koma Kankia bayan da aka samu yarjejeniyar zaman lafiya a wasu ƙananan hukumomi maƙwabta, lamarin da ya sa suka faɗaɗa hare-harensu zuwa yankunan Charanchi da Kusada.

Wani mazaunin yankin mai suna Haladu Badole ya ce: “Kwana uku da suka gabata mun fara lura da motsin wasu mutane da ba mu saba gani ba, sannan a daren jiya suka kai hari suka kwashe dabbobinmu.”

Mutanen yankin sun roƙi hukumomi da su tura jami’an tsaro domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Yankin gabashin Kankia, ya kasance cikin zaman lafiya, sai dai kwanan nan an fara samun hare-hare a yankunan Rimaye, Magam, Sukuntuni, Gyaza da Kunduru.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Sadik Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Amma ya ce rundunar ta fara bincike kuma tana ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *