Na yi nadamar rashin aiwatar da dokar kwarmato kan masu satar kuɗi — Adeosun

[ad_1]



Tsohuwar Ministar Kuɗi a Najeriya, Kemi Adeosun, ta bayyana cewa tana nadamar rashin aiwatar da dokar kwarmato  yadda ya kamata domin yaƙar satar kuɗaɗen gwamnati.

A wata tattaunawa da ’yan jarida, Adeosun ta ce gazawarta wajen tabbatar da cikakken aiki da wannan doka ta whistleblower policy ta janyo babban giɓi a yaƙin da Najeriya ke yi da cin hanci da rashawa.

Ta bayyana cewa dokar kwarmato na da matuƙar muhimmanci wajen tona asirin badaƙala, musamman a harkokin mu’amalar kuɗaɗen gwamnati, amma rashin aiwatar da ita yadda ya dace ya rage tasirinta.

A cewarta, da an inganta tsarin kariya ga masu fallasa rashawa tun da wuri, da an samu gagarumin ci gaba wajen daƙile satar dukiyar jama’a.

Ta kuma jaddada cewa kare masu kwarmato da ba su kariya yana da muhimmanci domin karfafa gwiwar jama’a su riƙa fallasa duk wani aikin rashin gaskiya a hukumomin gwamnati.

Adeosun ta ƙara da cewa dole ne gwamnati ta ɗauki darasi daga baya domin inganta dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da ana aiwatar da su ba tare da son kai ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *