HOTUNA: Yadda dandazon jama’a suka cika tituna yayin dawowar Gwamnan Kano
[ad_1]
Dubban jama’a ne suka fito kan manyan titunan Kano a ranar Asabar domin tarbar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bayan dawowarsa daga wasu taruka da shugabannin jam’iyyar APC a Abuja.
Rahotanni sun ce gwamnan ya kasance cikin tawagar APC da ta je Jihar Bauchi domin zawarcin Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP zuwa APC.
Magoya bayan gwamnan sun mamaye hanyoyi tun daga mashigar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano har zuwa Kofar Mata zuwa Gidan Gwamnati, suna kaɗa tutoci tare da rera waƙoƙin goyon baya.

Masu alaƙa
[ad_2]
Source link