Magidanta 96 sun yi watsi da ’ya’yansu babu kulawa a 2025 a Gombe — NHRC

[ad_1]



Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC), ta ce magidanta 96 ne suka yi watsi da ’ya’yansu a Jihar Gombe a shekarar 2025.

Kakakin hukumar a Gombe, Mista Ali Alola-Alfinti ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan rahoton shari’o’in take haƙƙin ɗan Adam a hukumar.

Ya ce gaba ɗaya shari’o’i 285 aka samu a shekarar, inda barin yara babu kulawa ya fi yawa.

A cewarsa, sauran shari’o’in sun haɗa da:

  • shari’o’i 59 na cin zarafi
  • 36 na take haƙƙin dukiya
  • 16 na hana mutane samun adalci
  • 14 na barazana ga rayuwa
  • da kuma shari’o’i 6 na rikici kan rainon yara.

Alola-Alfinti, ya ce daga cikin shari’o’i 285, hukumar ta samu nasarar warware 256 tare da taimakon wasu hukumomin gwamnati, yayin da ake ci gaba da bincike kan sauran a shekarar 2026.

Ya yi kira ga iyaye, musamman maza, da su kula da ’ya’yansu yadda ya kamata, yana mai cewa barin yara babu kulawa babban take haƙƙi ne da ke hana su samun ilimi, lafiya da rayuwa mai kyau.

Ya ƙara da cewa yawan irin waɗannan shari’o’i na raguwa sakamakon wayar da kan al’umma da NHRC ke yi tare da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.

Kakakin ya yi gargaɗin cewa barin yara kan haddasa matsalolin tunani kamar rashin yadda da kai, damuwa da munanan halaye, tare da roƙon iyaye su kare lafiyar ’ya’yansu da makomarsu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *