Mutum 7 sun rasu yayin da tirela ta murƙushe motoci a Madalla

[ad_1]



Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu, yayin da wasu guda biyar suka ji rauni bayan wata tirela ta murƙushe motoci biyu a yankin Madalla, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, a Jihar Neja.

Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Juma’a, lokacin da wata tirela ta samu matsalar birki, ta yi awon gaba da wasu motoci biyu.

Wani ganau, Saleh Haruna, ya ce kafin aukuwar hatsarin, direban wata motar bas ya bugi wata mota a gabansa, wanda hakan ya haddasa hatsaniya.

A cewarsa, a lokacin ne tirelar ta taho da sauri ta murƙushe su, hakan ya sa wani ɓangare na bas ɗin ya kama da wuta.

A sakamakon haka, mutum huɗu da ke cikin bas ɗin sun ƙone ƙurmus, yayin da sauran suka samu rauni.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Lukas da ke Madalla, inda Dakta Ugwoegbu Valentine, ya tabbatar da rasuwar ƙarin mutum uku daga cikin waɗanda suka ji rauni.

Direban tirelar, Sulaiman Rabiu, ya shaida cewa ya taso daga Warri, a Jihar Delta, yana ɗauke da buhun alkama waɗanda zai kai Kano.

Ya ce lokacin da yake saukowa daga Madalla ne birkin motarsa ya ƙi aiki, lamarin da ya janyo hatsarin.

Rundunar ’yan sandan yankin Madalla ta tabbatar da rasuwar mutum bakwai a hatsarin.

Sai dai jama’a a yankin sun koka kan yadda aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna ke tafiya.

Sun zargi kamfanin da ke aikin da gazawa wajen saka alamomi da samar da wuraren tsayawar fasinjoji da motoci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *