Hakkin Ma’aurata A Kan Junansu (2)

[ad_1]

…cigaba daga makon da ya gabata

9• Mace ta rinka gaggawar bawa mijinta hakuri a duk lokacin data yi masa laifi, shima kada yayi girman kai ya amsa mata, haka kuma idan yayi mata laifi shima ya rinka bata hakuri, hakan yana kawo soyayya mai karfi da kuma zuri’ah mai kyau.

10• Mace ta zama mai kyakkyawan hali ga mijinta, kaima kazama mai kyawawan hali ga matarka.

11• Miji ya maida matarsa abokiyarsa, itama ta rika abota da mijinta su rinka hirar soyayya akoda yaushe.

12• Miji ya ringa goyo matarsa idan itama za ta iya ta ringa goya mijinta lokaci-lokaci.

13• A lokaci zuwa lokaci ku rika wasa da junanku.

14• Ka rinka yi mata murmushi a duk lokaci data kalleka, haka kema ki rinka masa murmushi a duk lokcin daya kalleki.

15• A duk lokacin ku rinka nunawa juna farin ciki da nuna jin dadin juna, ku kuma rinka kokarin yadda za ku shako da junanku, kowa ya rinka nuna damuwarsa idan daya baya tare dashi.

16• Ki rinka yiwa mijinki addu’a a duk lokacin da kikai sallah, kina masa fatan alkhairi, kaima ka rinka yiwa matarka addu’a kana yi mata fatan alkahiri aduk lokacin da kayi sallah.

17• Idan ka fita aiki ko kasuwa ka rinka kiranta kana jin muryarta kana kuma yi mata godiya da yadda take hakurin zama a gida kana yaba mata.

Kema ki rinka kiransa kina gaisheshi kina masa fatan alkhairi, kina kwantar masa da hankali.

18• Idan mijinki yadawo ki tareshi da murna da farin ciki, ki kuma karbi abinda ke hannunsa.

Kaima kashigo kana mai murmushi da farin ciki kuma katari matarka kana mai nuna mata farin ciki.

19• Sannan miji ya rinka neman shawara a gurin matarsa, itama ta rinka shawara da mijinta akan wasu kebantattun lamura.

20• Sannan ku rinka taimakawa matanku da ‘yan kudade, wanda yake da hali ya saka mata albashi, wanda baida hali kuma yarinka yi mata kyauta na kudi lokaci-lokaci saboda tana iya yin baki wadannan kudade za su taimaka mata wajen fitar daku kunya kai da ita.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *