DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba
[ad_1]
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta kama wasu tsoffin jami’anta biyu da ta kora daga aiki bisa zargin yin amfani da sunan hukumar wajen aikata zamba.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana sunayen mutanen da aka kama da Barry Donald da Victor Onyedikachi Godwin.
DSS ta ce mutanen na amfani da sunanta suna yaudarar jama’a.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kama su, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abin da suka aikata.
A baya, DSS ta gargaɗi jama’a cewa waɗannan mutane ba su da alaƙa da hukumar, domin an kore su daga aiki, kuma duk wani abu da suke yi ba ya da nasaba da DSS.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link