He Lifeng Ya Halarci Taron WEF Tare Da Ziyartar Kasar Switzerland
[ad_1]
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar, He Lifeng ya halarci taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na WEF, a jiya Talata 20 ga wata a birnin Davos na kasar Switzerland.
A gun taron, He Lifeng ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana ra’ayoyinsa guda hudu. Wato na farko, ya kamata a tsaya tsayin daka kan goyon bayan ciniki mai ‘yanci, kuma a hada karfi da karfe wajen ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya. Na biyu, ya kamata a tsaya tsayin daka kan kiyaye cudanya a tsakanin mabambantan bangarori, tare da inganta tsarin tattalin arziki da ciniki na duniya ta yadda zai zama mai karin adalci. Na uku, ya kamata a tsaya tsayin daka kan hadin gwiwar moriyar juna, a fadada hadin gwiwa tare da hada hannu da juna wajen daidaita matsalolin ci gaba da ake fuskanta. Na hudu, ya kamata a tsaya tsayin daka kan martaba juna da daidaita sabani ta hanyar shawarwari. He Lifeng ya kuma yi karin haske game da cikakken zama na hudu na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, inda ya jaddada cewa, bunkasuwar kasar Sin za ta samar da muhimman damammaki ga duniya.
A yayin taron, He Lifeng ya kuma gana da shugaban tarayyar Switzerland, Guy Parmelin, da mataimakin shugaban kasar Ignazio Cassis.
[ad_2]
Source link