Jami’ai Biyu Sun Mutu A Ƙunar Baƙin Wake A Moscow
[ad_1]
Jami’an ‘yansanda biyu sun mutu a cikin wani harin ƙunar baƙin wake da ta faru cikin dare a Moscow yayin da jami’an suka yi ƙoƙarin tsayar da wani mutum da ake zargi, in ji Kwamitin Bincike na Rasha a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Fashewar ta faru ne kusa da wurin da aka kashe wani janar ɗin soja na Rasha a farkon wannan makon.
“An tayar da wani abun fashewa” yayin da jami’an suka kusanci wanda ake zargi, wanda ke kusa da motar sintirinsu, in ji sanarwar kwamitin, wanda ke binciken manyan laifuka.
Lamarin wanda aka sanar a Telegram ta ce, masu bincike suna duba wurin da abin ya faru don fara gudanar da binciken asalin abin da ya faru na fashewar bam ɗin.
[ad_2]
Source link