Sojoji sun tarwatsa ’yan ta’adda, sun kama mutum 5 da makamai a Yobe

[ad_1]



Sojojin Operation Hadin Kai, sun tarwatsa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a yankin Mangari, tare da cafke mutum biyar da ake zargi da safarar makamai da satar mutane.

Majiyoyin tsaro sun ce da misalin ƙarfe 6:21 na yammacin ranar 17 ga watan Fabrairu, sojoji sun kai samame bayan sun samu bayanan sirri cewa wasu ’yan ta’adda sun taru a yankin Mangari.

Bayan zuwan sojojin, waɗanda ake zargin suka tsere, lamarin da ya kawo cikas ga shirinsu.

A wani samame na daban, sojoji sun kama wasu mutum biyar da ake zargi da safarar makamai da garkuwa da mutane.

An kama su ne da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar ranar 18 ga watan Fabrairu a shingen bincike da ke kan hanyar Gombe zuwa Potiskum.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Baba Abare mai shekaru 41, wanda aka samu da bindiga ƙirar AK-47.

Sauran da aka kama shi da su, sun haɗa da Idris Zakari (33), Nasiru Aliyu (25), Abdullahi Sulaiman (35) da Mohammed Idris (34), dukkaninsu ’yan asalin Potiskum ne.

An kama su ne a cikin motoci ƙirar Golf Wagon guda biyu masu lambar Borno NGL-506XA da Kaduna DKD16-01.

Sojoji sun ƙwace makaman sannan sun miƙa waɗanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *