Ba ma tsoron karawa da Maroko — Osimhen




Ɗan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen, ya ce tawagar Super Eagles ba ta tsoro ko fuskantar matsin lamba kafin karawarsu da ƙasar Maroko a wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025.

Najeriya za ta fafata da Maroko, wacce ita ce mai masaukin baƙi, a daren ranar Laraba a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.

Duk da cewa ana sa ran filin zai cika da magoya bayan Maroko a matsayinta na mai masaukin baƙi, Osimhen ya ce hakan ba zai razana Super Eagles ba.

Osimhen, ya bayyana cewa ’yan wasan Najeriya suna da natsuwa kuma sun mayar da hankali ne kawai kan abin da ya kamata su yi a fili.

Ya ce ba sa ɗaukar karawa da Maroko a matsayin barazana, illa face suna buga wasa ne mataki-mataki.

Ya cd Maroko tana da ’yan wasa ƙwararru, amma ya jaddada cewa Najeriya ta riga ta nuna irin ƙwarewarta don lashe kofin bayan doke Algeriiya a wasan da ya gabata.

A cewarsa, da dama daga cikin ’yan wasan Super Eagles sun saba da buga wasa a manyan filayen wasa cike da dubban magoya baya.

Ɗan wasan Napoli ya ce tawagar za ta yi duk mai yiwuwa domin samun nasara, yana mai cewa Najeriya ba ta tsoron kowa kuma tana da kwarin gwiwar lashe kofin.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *