Gwamnatin Katsina Ta Biya Bashin Kuɗin Giratuti Na Naira Biliyan 12 — NULGE
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Katsina ta warware tarin bashin giratuti da ya kai Naira Biliyan 12, wanda hakan ya rage wa ma’aikatan kananan hukumomi da suka yi ritaya kalubalen rayuwa a Jihar.
Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE), Kwamared Nasir Wada Mai adua, ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da LEADERSHIP a ofishinsa.
Ya bayyana wannan ci gaban a matsayin babban taimako ga masu fansho da iyalan ma’aikatan da suka rasu a fadin jihar, ya kara da cewa, biyan wannan bashin na daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin yanzu ta samu a fannin walwalar ma’aikata.
“Katsina a zahiri jiha ce ta ma’aikata inda kusan kashi 90 cikin 100 na mutanenta, suka dogara da albashi, da fansho. Biyan wannan kudaden babban ci gaba ne,” in ji shi.
[ad_2]
Source link