HOTUNA: Jana’izar ɗaliban makaranta da harin Amurka da Isra’ila ya kashe a Iran
[ad_1]
Ana gudanar da jana’izar aƙalla mutane 165, galibinsu ƙanana ‘yan mata, waɗanda suka rasa rayukansu a mummunan harin da Amurka da Isra’ila suka kai Iran a ranar Asabar.
Ana iya tuna cewa, wasu daga hare-haren da aka ƙaddamar sun faɗa kan wata babbar makarantar mata ta Shajareh Tayyebeh Girls’ Elementary School a garin Minab da ke lardin Hormozgan, a lokacin da darussa ke gudana.
A jiya Litinin ce Gwamnan Minab ya ce an gama ayyukan ceto a wurin kuma an gano gawarwaki 165 a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da suka rushe, yayin da wasu mutane 96 suka ji raunuka.
Mahukuntan Iran dai sun bayyana harin a matsayin mummunan laifi wanda suke nanata cewa “ba za a ƙyale ba tare da martani ba.”
Masu alhini sun yi dandazo a garin Minab, inda ake jana’izar ɗalibai da ma’aikatan makarantar firamaren ta lardin Hormozgan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu wanda ke da haƙƙin mallakar hotunan ya nuna yadda aka yi wa akwatunan gawarwakin lulluɓi da tutocin ƙasar ta Iran a yayin jana’izar.




Masu alaƙa
[ad_2]
Source link