Ronaldo Ya Fice Daga Saudi Arabia Yayinda Hare-Haren Kasar Iran Suka Zafafa
[ad_1]
Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr, Cristiano Ronaldo, ya tashi daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya a tsakiyar Dare, yayinda hare hare ta sama da Iran ke kaiwa kasar ya zafafa, an ruwaito cewar jirgin Ronaldo ya bar kasar Saudiyya zuwa inda ake kyautata zaton birnin Madrid na kasar Sifaniya.
Ficewar Ronaldo daga Saudiyya ta zo ne a daidai lokacin da rikici ke kara kamari a Gabas ta Tsakiya, Ronaldo mai shekaru 41 ya tashi zuwa Madrid a kasar Sifaniya a cikin jirginsa na kashin kansa mai darajar fam miliyan 61, na’urar dake bin diddigin jirgin ta bayyana cewa jirgin Bombardier Global Express na Ronaldo ya yi tafiyar kusan awanni bakwai zuwa birnin Madrid, jirgin mai tsada ya tashi da karfe 8 na dare kuma ya isa da misalin ƙarfe 3 na safiya.
Ronaldo, wanda kungiyarsa ke fafutukar lashe gasar, yana zaune a birnin Riyadh birnin da bama-baman Iran suka afkawa yayin da aka shiga kwana na hudu ana musayar wuta tsakanin kasashen Isra’ila dake samun tallafin Amurka da kuma kasar ta Iran, Ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh ya fuskanci hare-haren jiragen sama marasa matuka guda biyu cikin dare, kuma kafofin watsa labaran gwamnatin Iran sun yi iƙirarin cewa an lalata wani ginin ofishin da kuma wata ma’aikata a Bahrain.
[ad_2]
Source link