PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote

[ad_1]



Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote.

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba.

Ƙungiyar ta kuma gargaɗi matatar Dangote da kada ta kaeya yarjejeniyar da aka cimma a ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro.

Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, wanda ya sanar da janye yajin aikin, ya ce idan matatar ta karya yarjejeniyar, ƙungiyar ba za ta yi shiru ba.

Rikicin ya samo asali ne bayan wasu ma’aikatan matatar Dangote sun shiga ƙungiyar PENGASSAN, lamarin da ya haddasa rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.

Yajin aikin ƙungiyar ya haifar da tsoron samun ƙarancin man fetur da gas a faɗin Najeriya.

Har ila yau, ƙungiyar ta yi barazanar daina kai wa matatar Dangote mai, lamarin da ka iya zama babbar barazana ga harkar man fetur a Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *