An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

[ad_1]


An gudanar da taron musamman na tattaunawa tsakanin sassan kasa da kasa mai taken “kirkira, bude kofa da more ci gaba” a jiya Litinin a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, wanda babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya shirya.

Taron ya tattaro sama da manyan baki mahalarta 100 daga fannoni daban-daban na siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da ilimi, da kafofin watsa labarai na Sin da Afirka ta Kudu, don tattaunawa mai zurfi kan yadda Sin ke fadada bude kofa mai girma ga duniya, da kuma hadin gwiwa don gina makoma mai wadata tare.

Shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce an rufe cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS a kwanan baya a Beijing, wanda ya jawo hankulan duniya sosai, wanda kuma ya nuna wani muhimmin ci gaba a zamani da Sin ta samu. Ya kara da cewa, a karkashin sabon daftari, Sin za ta ci gaba da bude kofarta, da samar da damammaki masu yawa ga duniya. A daya bangaren, CMG za ta yi amfani da karfinta na watsa labarai ga duniya, don ba da labaran Sin da kyau, domin nuna damammaki masu yawa na kasar, da kuma raba fa’idodin ci gaban Sin na zamani tare da duniya.

A nasa bangare kuwa, ministan kimiyya da kirkira na Afirka ta Kudu, Dr. Blade Nzimande, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, ya gamsu da babban nasarar da Sin ta samu a wa’adin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14. Ya ce, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba mai karfi ba tare da tangarda ba, kuma yana karawa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa.

Ya ce Afirka ta Kudu tana fatan koyi daga sabon tsarin ci gaban Sin, don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka shafi sauyin yanayi, da tattalin arzikin dijital, da fasahar sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *