Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim
[ad_1]
Daya daga cikin Dattawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood wanda ya shade tsawon lokaci ana fafatawa dashi a harkar, Tanimu Akawu ya bayyana cewar tunda yake harkar fim sau Daya ne kadai ya taɓa da-nasanin fitowa a cikin shirin fim.
Tanimu a wata hira da yayi da BBC Hausa a cikin shirinsu na Daga Bakin Mai Ita ya ce akwai wani fim da ya taba fitowa a matsayin sangartaccen Yaro duk da girman shekarun da yake dasu mai suna Dan Fari, sai bayan an kammala aikin daukar fim din ne ya gano cewar ya tabka kuskure domin kuwa masoyansa da dama basu jin dadin hakan ba.
Da yake amsa tambaya akan abinda yasa yawancin fina finansa yake fitowa a matsayin mutum mara tausayi (Villain) Tanimu yace ya sha yiwa Furodusoshi wannan tambaya amma sai suka ce abinda yafi dacewa dashi kenan dole ya hakuri da wannan role din.
Daga karshe Tanimu Akawu ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim da su kasance masu hakuri kada suyi hassada kuma su dage da addu’oi, Harkar fim sana’ace da ake samun rufin asiri da daukaka, kuma fim sana’ace wadda sai dai kai ka barta ba dai ta barka ba.
[ad_2]
Source link