Atiku ya karyata ba sojan da ya yi takaddama da Wike kyautar motar SUV

[ad_1]



Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta ba tare da wata hujja ba.

Ibe ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labari da aka ƙirƙira.

“Mai girma Atiku Abubakar, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Najeriya (1999–2007), bai bai wa Laftanar Ahmed Yerima, ko wani mutum ba, sabuwar motar Toyota SUV, sabanin rahotannin ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta.

“Labarin ƙarya ne gaba ɗaya kuma ya kamata jama’a su yi watsi da shi,” in ji shi.

Zargin da ya fara yawo a Facebook a ranar Laraba ya ce Atiku ya ba da kyautar motar ga sojan ruwa bayan takaddamar da ya samu da Wike kan wani rikicin fili a Abuja.

Takaddamar ta faru ne a ranar Talata lokacin da Wike ya yi arangama da sojan ruwan yayin da yake duba wani fili da ake takaddama a kan shi a unguwar Gaduwa da ke cikin Babban Birnin Tarayya.

Bidiyon lamarin da ya yadu a intanet ya nuna yadda aka yi musaya yawu mai zafi tsakanin ministan da sojan.

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a fadin ƙasa, inda fitattun mutane da dama, ciki har da tsohon Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Janar Tukur Buratai (mai ritaya), da wasu ’yan siyasa, suka bukaci a kai zuciya nesa kuma a girmama dokokin kasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *