Zargin Karkatar Da Biliyoyin Naira: Kotun Kano Ta Sake Ɗage Shari’ar Ganduje

[ad_1]

A ranar Talata, wata Babbar Kotun Jihar Kano ta dage shari’ar har zuwa ranar 15 ga Afrilu, 2026, inda za a saurari ƙorafe-ƙorafe na farko da duk wasu abubuwa da ake jira a shari’ar, wacce ake zargin an yi sama da faɗi da dukiyoyin al’umma wacce ake zargin tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Ganduje, da wasu mutane bakwai.

An dage shari’ar ne bayan samun jinkiri a yayin gudanar da shari’ar, inda manyan lauyoyi biyar (SANs) da ke jagorantar shari’ar basu samu halarta ba sai dai wakilansu.

LEADERSHIP ta ruwaito a baya cewa, Gwamnatin Jihar Kano ta gabatar da tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, makirci, almubazzaranci da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai biliyoyin naira a kan Ganduje da matarsa, Hafsat Umar.

Sauran waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited da Lasage General Enterprises Limited.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *