Kotu ta ɗaure wani mutum kan kashe saurayin ’yarsa a Ekiti

[ad_1]



Wata kotu a Jihar Ekiti, ta tura wani mutum mai suna Ibrahim zuwa gidan yari bisa zargin kashe saurayin ’yarsa.

Rahotanni sun ce saurayin ya ziyarci budurwarsa a gidan mahaifinta da ke kusa da Corpers’ Lodge, a kan titin New Iyin, Ado Ekiti.

Mahaifin, wanda ba ya son dangantakaru, ya kira ’yan uwansa suka tare saurayin, inda suka yi masa dukan da ya yi sanadin mutuwarsa saboda zubar jini.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da gurfanar da mahaifin yarinyar.

Hakazalika, ya ce an gurfanar da wasu mutane biyu, kuma kotu ta tura su gidan yari yayin da ake ci gaba da shari’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *