Boko Haram ba kiristoci kaɗai suke kashewa a Arewa Maso Gabas — Ndume

[ad_1]



Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya ce ba daidai ba ne a riƙa cewa Boko Haram Kiristoci kawai suke kashewa a Arewa maso Gabas.

Ya bayyana cewa ƙungiyar tana kai wa Musulmi da Kiristoci hare-hare baki ɗaya, don haka bai kamata a alaƙanta ta da addini ɗaya ba.

Ndume, ya mayar da martani ne kan wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa wanda ta yi iƙirarin cewa dukkanin waɗanda aka kashe kwanan nan a hare-haren Boko Haram Kiristoci ne.

Ya ce a hare-haren da suka faru a ƙarshen mako a Jihar Borno, Musulmi biyar aka kashe a ƙauyen Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a ranar Asabar.

Sannan an kashe Kiristoci uku a ƙauyen Mussa na Karamar Hukumar Askira-Uba a ranar Lahadi.

Sanatan ya yi gargaɗin cewa yaɗa irin wannan labari yana da hatsari domin yana iya raba kan jama’a, yana rage wa sojojin da ke yaƙi da ta’addanci ƙwarin guiwa, kuma ya iya kawo mummunan sakamako.

Ya ce Boko Haram ba sa kallon addini ko ƙabila, domin kai wa talakawa hare-harensu, waɗanda kawai suke neman zaman lafiya da yin noma.

Ndume ya yaba wa sojoji bisa jajircewarsu wajen yaƙi da ’yan ta’addan, amma ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara kula da walwalar sojojin tare da samar musu da isassun makamai domin su samu damar yaƙar Boko Haram.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *