Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa kan kashe tsohuwar matarsa a Gombe




Babbar Kotun Jihar Gombe, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 25, Hassan Mohammed, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe tsohuwar matarsa, Halima Sadiya Adamu.

Hassan Mohammed ɗan asalin ƙauyen Falangaya ne, da ke Ƙaramar Hukumar Dukku a Jihar Gombe.

Mai shari’a Abdulhamid Mohammed Yakubu na Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba ta biyu ne, ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da laifin kisan.

Kotun ta ce laifin ya saɓa da sashe na 221 na Dokar Penal Code.

A cewar ɓangaren gwamnati, lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Maris, 2025, da misalin ƙarfe 1 na rana.

An zargi Hassan da kai wa tsohuwar matarsa hari da wuƙa tare da yanka a wuya, bayan ta ƙi amincewa ta sake aurensa.

Daraktan shari’a na gwamnati (DPP), Barrista Abubakar Jungudo, wanda ya jagoranci ɓangaren masu gabatar da ƙara a madadin gwamnatin jihar, ya ce laifin ya saɓa wa Sashe na 221 na Dokar Penal Code.

Lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen da ake masa, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin.

A yayin shari’ar, ɓangaren gwamnati sun gabatar da shaidu shida da suka bayar da shaida kan abin da suka gani lokacin da lamarin ya faru.

Haka kuma kotu ta karbi wukar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin a matsayin hujja.

Lauyan wanda ake tuhuma, Barrista Habib Alkali, ya yi wa shaidun gwamnati tambayoyi domin tantance shaidarsu.

Daga bisani ɓangaren kariya ya gabatar da wanda ake tuhuma a matsayin shaidarsa ɗaya tilo, inda ya sake musanta aikata laifin.

Sai dai ɓangaren gwamnati sun sake yi masa tambayoyi.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Yakubu, ya ce ɓangaren gwamnati sun tabbatar da laifin kisan kai a kan wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba.

Saboda haka kotun ta same shi da laifin kashe tsohuwar matarsa ta hanyar yanka mata wuya da wuƙa.

Sannan ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda Sashe na 221 na Dokar Penal Code ya tanada.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *