Saka Wasu Kamfanonin Japan Cikin Jerin Kamfanonin Da Aka Hana Sayar Musu Da Kayayyakin Sin Mataki Ne Da Ya Dace

[ad_1]

Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta kira taron manema labarai a yau Alhamis 26 ga watan Fabrairu, inda mai magana da yawunta, He Yongqian, ta amsa tambayar da ta shafi kasar Japan, tana mai cewa, kasar Japan ta gaggauta kara karfin soja da shirya makamaiSaka Wasu Kamfanonin Japan Cikin Jerin Kamfanonin Da Aka Hana Sayar Musu Da Kayayyakin Sin Mataki Ne Da Ya Dace a kwanan nan, al’amarin da ya nuna yunkurinta mai hadarin gaske na sake farfado da ayyukan soja da mallakar makaman nukiliya, wanda zai haifar da barazana ga zaman lafiyar shiyyar da ma duniya baki daya.

A cewar kakakin, saka wasu daidaikun kamfanonin kasar Japan cikin jerin sunayen kamfanonin da aka hana sayar musu da kayayyakin kasar Sin, da kasar ta yi a ranar 24 ga watan Fabrairu, mataki ne da aka dauka da nufin hana yunkurin Japan na sake bunkasa karfin soji da mallakar makaman nukiliya, wanda ya yi daidai kuma ya dace da doka.

Kazalika, yayin amsa tambayar da ta shafi shawarwarin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da Amurka zagaye na shida, wadanda za su gudana nan ba da jimawa ba, He Yongqian ta ce, kasarta na son yin kokari tare da bangaren Amurka, wurin aiwatarwa gami da kiyaye matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin ganawarsu a Busan da tattaunawarsu ta waya a ranar 4 ga watan Fabrairu, da daidaita sabanin ra’ayi, da fadada hadin gwiwa ta hanyar yin shawarwari, domin daukaka ci gaban dangantakarsu ta bangaren tattalin arziki da kasuwanci mai dorewa kuma ta hanyar da ta dace, da kara amfanar da kasashensu har ma da duk duniya baki daya. (Murtala Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *