Babakeren Amurka Ya Zama Ta’Addanci Irin Na Siyasa A Duniya

[ad_1]

Kutsawa cikin wata kasa mai cikakken ikon mulki ba tare da kunya ba, da kuma tsare shugaban wata kasa, bisa yadda Amurka ta nada kanta “’Yar sanda da alkaliya ta kasa da kasa”, mataki ne na keta dokokin kasa da kasa, da ka’idojin dangantakar kasa da kasa.

Babakeren Amurka ya bayyana ainihin fuskarta: wato aiwatar da mulkin mallaka, da cin nasara da karfin tuwo da kuma kwace albarkatu. Binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta babban rukunin gidan gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ta gudanar ga masu amfani da intanet a dukkanin fadin duniya, ya nuna yadda kaso 93% na wadanda aka bincika suka amince Amurka ta yi babakere, duba da yadda ta tattake ikon mallakar yankin kasar Venezuela, kuma kaso 91.7 % sun nuna damuwa mai zurfi game da kunnon kan “ta’addanci na kasa” na Amurka.

A cikin binciken, kashi 92.8% na wadanda aka bincika suna ganin cewa, amfani da karfin tuwo da Amurka ta yi kan Venezuela, ya keta tsarin ikon mallakar kasar, kuma kashi 89% suna ganin cewa, harin da gwamnatin Trump ta kai wa Venezuela, babu adalci da halasci a cikinsa. Kana kaso 94.3% na ganin cewa, ainihin manufar bangaren Amurka ita ce kwace albarkatun mai daga Venezuela. Kazalika, kaso 86.6% na damuwar cewa yawancin kasashen Latin Amurka da Caribbean na fuskantar irin wannan hadari da ya faru a kasar Venezuela, dadin dadawa kashi 87.8% na bayyana cewa, wannan matakin da Amurka ta dauka barazana ce sosai ga zaman lafiya da tsaro a yankin Latin Amurka da Caribbean. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *