Bayan Taka Nakiya, Sojoji 9 Sun Rasu, Wasu Sun Raunata A Borno

[ad_1]

An ruwaito cewa sojoji tara sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka daban-daban lokacin da wani ayarin motocin sojoji ya taka nakiya a Bindundul, kusa da Kareto, a yankin karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce, sojojin suna kan hanyarsu ne daga Maiduguri zuwa Damasak, hedikwatar karamar hukumar Mobbar, lokacin da lamarin ya faru a ranar Lahadi da yamma.

  • An kashe ‘Yan Ƙasarmu 32 A Lokacin Mamayar Amurka A Venezuela — Gwamnatin Cuba
  • Babakeren Amurka Ya Zama Ta’Addanci Irin Na Siyasa A Duniya

Majiyar ta kara da cewa, sojojin sun tsaya a wani shingen soji a kan hanya a ranar Asabar don hutawa, sannan suka ci gaba da tafiyarsu washegari.

Majiyar ta kara da cewa, motar sojoji mai jure harin bam ta lalace matuka yadda ba za ta gyaru ba saboda ƙarfin fashewar bam din.

An tabbatar da cewa, sojoji da dama sun samu raunuka a lokacin fashewar nakiyar, inda daga baya wasansu suka rasu.

“Sojoji takwas sun mutu a ranar Lahadi daga cikin wadanda suka jikkata, yayin da wani daya ya mutu a safiyar yau (Litinin),” in ji majiyar, wanda ya kawo adadin waɗanda suka rasu zuwa tara.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *