An gurfanar da Maduro a Kotun Amurka

[ad_1]



Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro, tare da matarsa Cilia Flores, sun bayyana a gaban wata kotun tarayya a birnin New York, domin fuskantar shari’a bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, ta’addanci, da mallakar manyan makamai masu haɗari.

Lamarin wanda shi ne karo na farko da Maduro ke bayyana a gaban kotu na zuwa ne kwanaki biyu bayan sojojin Amurka sun kama su a ranar 4 ga Janairu, 2026 a Caracas, babban birnin Venezuela, a wani farmaki da kawo yanzu ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a duniya.

Hukumomin Amurka sun sauya wa Maduro wuri daga gidan yarin tarayya da ke Brooklyn zuwa kotun tarayya da ke Manhattan, inda ya gurfana a gaban Alkali Alvin K. Hellerstein.

Maduro, mai shekaru 63, na fuskantar zargin jagorantar wata babbar ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi da ake zargin ta shigar da hodar iblis zuwa Amurka tsawon shekaru. Gwamnatin Amurka ta ce kudaden da aka samu daga wannan haramtacciyar harkar ne suka taimaka wajen ɗorewar mulkinsa.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Maduro

A cikin wata takardar tuhuma da Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta fitar, an zargi Maduro da safarar miyagun ƙwayoyi a matakin ƙasa da ƙasa, shirya ayyukan ta’addanci, mallaka da safarar manyan makamai masu haɗari, da kuma haɗin baki wajen aikata manyan laifuffukan tsaro.

Takardar ta kuma ƙunshi sunan matarsa, Cilia Flores, wadda ita ma za ta fuskanci irin waɗannan tuhume-tuhume.

Babbar Lauyar Ƙasa a Amurka, Pam Bondi, ta ce Maduro da matarsa za su fuskanci cikakken hukunci ƙarƙashin dokokin Amurka, tana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sassauci kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba.

Ana sa ran za a ci gaba da tsare Maduro a gidan yarin tarayya da ke Brooklyn, yayin da ake jiran fara shari’arsa gaba ɗaya.

Halin da ake ciki a Venezuela

A halin da ake ciki a Venezuela kuwa, an shirya rantsar da Delcy Rodríguez a matsayin shugabar riƙo. Kafin taron rantsuwar da za a gudanar a majalisar dokokin ƙasar, Rodríguez ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewa gwamnatinta na da niyyar ƙulla alaƙa mai mutuntaka da haɗin gwiwa da Amurka.

Sai dai Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada cewa Amurka ce ke da iko a halin yanzu kan Venezuela, wani furuci da ya ƙara tayar da hankula.

Rodríguez, wadda ake kallon ta a matsayin ta hannun daman Maduro, ta ce duk da halin da ake ciki, Maduro ne har yanzu shugaban ƙasar Venezuela, lamarin da ya janyo rashin tabbas kan sahihancin mulkin riƙon ƙwaryar.

Martani

Kamfanonin dillancin labarai na ƙetare sun wallafa hotunan da ke nuna yadda aka kai Maduro da matarsa cikin jirgi zuwa New York, tare da tsauraran matakan tsaro.

A yanzu haka, idanuwan duniya na kan martanin da Venezuela da ƙasashen Kudancin Amurka za su dauka, yayin da ake ci gaba da shari’ar da ke iya sauya alƙiblar siyasar ƙasar mai arzikin man fetur.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *