Iran ta ƙaryata iƙirarin Trump kan tattaunawa domin tsagaita wuta
[ad_1]
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce babu wata tattaunawa da ke gudana tsakaninta da Amurka, tana mai ƙaryata ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi “tattaunawa mai ma’ana” domin kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa na tattaunawa da wani babban jami’i daga Iran, inda ya kuma bayar da umarnin dakatar da shirin kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi na ƙasar na tsawon kwanaki biyar domin bai wa tattaunawar dama.
Sai dai Tehran ta mayar da martani da cewa wannan iƙirari wani yunƙuri ne na rage tashin farashin makamashi a kasuwannin duniya, tare da neman ƙarin lokaci domin aiwatar da shirinsa na soji.
Bayan sanarwar Trump a shafinsa na Truth Social cewa ya ɗage kai hari kan tashoshin wutar lantarki da kayan makamashin Iran da kwanaki biyar, farashin mai ya faɗi, yayin da kasuwannin kuɗi suka samu ƙarin darajar hannayen jari.
A gefe guda, Iran ta jaddada matsayinta kan Mashigar Hormuz, inda ta ce hanya guda da jiragen ruwa za su iya bi ita ce ta hanyar haɗin kai da ita,
Tehran ta tana mai cewa ba ita ce ta fara yaƙin ba, saboda haka duk wani kira na rage tashin hankali ya kamata a mayar da shi ga Washington.
Haka kuma, jami’an tsaron Iran sun yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na ƙara tsananta rikicin zai iya jefa yankin cikin matsanancin rikicin makamashi, musamman idan aka ci gaba da hana zirga-zirga a mashigar.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ya ɓarke tun daga ƙarshen watan Fabrairu ya riga ya janyo tashin farashin mai sama da dala 100 kan kowanne ganga, lamarin da ke barazana ga tattalin arzikin duniya.
Duk da haka, ƙasashe irin su Birtaniya sun ce duk wani rahoto da ke nuna yiwuwar tattaunawa tsakanin ɓangarorin na da muhimmanci, suna mai jaddada buƙatar a gaggauta kawo ƙarshen rikicin da kuma buɗe Mashigar Hormuz.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link