Ba za mu sassauta wa masu tayar da tarzoma ba — Iran

[ad_1]



Hukumomin ƙasar Iran sun bayyana cewa ba za su sassauta wa waɗanda suke tayar da tarzoma ba, duk da cewa ‘yan ƙasa na da ‘yancin gudanar da zanga-zanga cikin lumana.

Shugaban sashen shari’a na Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan shafe sama da mako guda ana ci gaba da zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar mutane a wasu wurare.

Wannan na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa Iran za ta “fuskanci mummunan hari daga Amurka” idan har hukumominta suka ci gaba da kashe masu zanga-zanga.

Asalin zanga-zangar

Zanga-zangar dai ta fara ne a ranar 28 ga Disamba, lokacin da ‘yan kasuwa a birnin Tehran suka tsunduma yajin aiki sakamakon tsadar rayuwa da durƙushewar tattalin arziki.

Daga bisani zanga-zangar ta bazu zuwa wasu sassan ƙasar, inda ta rikiɗe daga batun tattalin arziki zuwa buƙatun siyasa.

Umarnin kotu ga jami’an tsaro

A cewar Babban Jojin Iran, Mohseni Ejei, ya ba da umarni ga Babban Lauyan Ƙasa da dukkan masu gabatar da ƙara a faɗin Iran da su yi aiki da doka cikin tsanaki da tsauri kan masu tayar da tarzoma da duk wanda ke mara musu baya.

A cewarsa, “ba za a yi sassauci ko rangwame ga masu tayar da tarzoma da masu goyon bayansu ba.”

Sai dai ya ƙara da cewa gwamnati na sauraron koken masu zanga-zangar lumana, tare da bambance su da masu kawo hargitsi a cikin al’umma.

A ƙididdigar da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya fitar, zanga-zangar ta shafi larduna 25 cikin 31 na Iran, tare da bazuwa a aƙalla birane 45, mafi yawansu ƙanana ko matsakaita, musamman a yammacin ƙasar.

Rahotanni daga bangaren mahukunta sun tabbatar da cewa mutane aƙalla 12 sun mutu tun daga ranar 30 ga Disamba, ciki har da jami’an tsaro, sakamakon arangamar da aka samu a wasu wurare.

Matsin tattalin arziki

Babu shakka dai ƙasar Iran na fama da matsin tattalin arziki sakamakon takunkuman ƙasa da ƙasa, inda darajar kuɗin ƙasar ta faɗi da fiye da kashi ɗaya bisa uku idan aka kwatanta da dalar Amurka cikin shekara guda.

Haka kuma, hauhawar farashi na nan a mataki mai tsanani.

A ƙoƙarin rage wa jama’a raɗaɗin rayuwa, gwamnati ta sanar da biyan tallafin kuɗi na wata-wata ga kowane ɗan ƙasa, wanda ya kai kimanin kashi 3.5 cikin 100 na matsakaicin albashin wata.

Jaridar Arman Melli mai ra’ayin gyara ta ce gwamnati “ta saurari muryar masu zanga-zangar”, yayin da jaridun masu ra’ayin mazan jiya irin su Javan da Kayhan suka zargi Amurka da Isra’ila da ɗaukar nauyin masu tayar da tarzomar.

Barazanar Amurka da martanin Iran

Da yake magana da ‘yan jarida a cikin jirgin Air Force One, Shugaba Trump ya ce Amurka na sa ido sosai kan halin da ake ciki a Iran.

Ya bayyana cewa, “Idan suka (Iran) fara kashe mutane kamar yadda suka saba a baya, za su fuskanci mummunan martani daga Amurka.”

Shi ma Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ƙasarsa na goyon bayan “gwagwarmayar al’ummar Iran na neman ‘yanci.”

Sai dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baqaei, ya ce Isra’ila na ƙoƙarin rarraba kawunan jama’a da raunana haɗin kan ƙasa.

Halin da ake ciki a Iran

Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito cewa zanga-zangar ta ragu ƙwarai a daren Lahadi idan aka kwatanta da kwanakin baya.

A ranar Litinin, yawancin shaguna a Tehran sun buɗe, jama’a kuma sun koma harkokinsu bayan hutun ƙarshen mako na kwanaki huɗu.

Sai dai jami’an ‘yan sanda masu yaƙi da tarzoma sun bazu a manyan tituna, yayin da aka kafa jami’an tsaro a gaban wasu makarantu — wasu jami’o’i sun koma koyarwa ta yanar gizo kawai.

Haka kuma, an samu zanga-zangar goyon baya daga ‘yan Iran mazauna ƙasashen waje.

A wani gangami da aka gudanar a birnin Paris na Faransa, wata ‘yar asalin Iran mai suna Sahar Aghakhani, mai shekaru 29, ta ce: “Da kowace sabuwar zanga-zanga, mutanen Iran na ƙara matsawa gaba. A hankali, muna ƙara kusantar ƙarshen wannan mulki.”

A shekarun baya-bayan nan, Iran ta sha fuskantar manyan zanga-zangar ƙasa baki ɗaya, musamman a 2022, bayan mutuwar Mahsa Amini a hannun ‘yan sanda kan zargin karya dokar sanya hijabi.

Sai dai zuwa yanzu, zanga-zangar da ake ciki ba ta kai girman waccan ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *