Iran ta yi babban kuskure da ta zaɓi Mojtaba Khamenei sabon jagoran ƙasar — Trump

[ad_1]



Shugaba Donald Trump ya ce Iran ta yi babban kuskure da ta zaɓi Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran ƙasar bayan kashe mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei a harin da Amurka da Isra’ila suka kai.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, “Ina ganin sun yi babban kuskure” wajen zaɓen Mojtaba Khamenei a matsayin jagoran Iran.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Trump ya taɓa bayyana ɗan tsohon jagoran a matsayin “mutum mara tasiri” a fagen siyasa.

Haka kuma shugaban na Amurka ya ce “yanzu ya yi wuri a soma tattauna batu” kan yiwuwar ƙwace arzikin man fetur na Iran, amma ya ƙara da cewa bai ɗebe tsammani kan wannan yiwuwar gaba ɗaya ba.

Aminiya ta ruwaito cewa dubban magoya bayan gwamnati a ƙasar Iran a ranar Litinin sun fito kan titunan babban birnin ƙasar, Tehran, domin murnar naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar.

Hotuna daga wurin taron jama’a sun nuna mutane suna ɗaga hotunan Mojtaba da na mahaifinsa, Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a makon da ya gabata.

A wani hoto kuma, an ga wani mutum riƙe da allon da ke nuna kamar mahaifin yana miƙa tutar jagoranci ga ɗansa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *