Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 5 A Jihar Zamfara

[ad_1]

An kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga biyar a wani samame da rundunar Joint Task Force (JTF) ta kai a ƙaramar hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara.

Wannan na cikin wani saƙo da masanin harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.

  • Yaƙin Amurka Da Iran Na Iya Tura Farashin Litar Fetur Zuwa N2,000 A Nijeriya – PETROAN
  • Majalisar Dattawa Za Ta Gayyaci Kyari Kan Zargin Giɓin Kuɗi Har Naira Tiriliyan 210 A NNPCL

A cewarsa, jami’an tsaro sun yi arangama da ‘yan bindigar a lokacin samamen, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar da ake zargin ‘yan bindiga ne.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun kuma ƙwato wasu kayayyaki daga wajen da aka kai samamen.

Makama ya ce an gudanar da aikin ne a Kan Biri da ke wajen garin Kwaren Ganuwa a ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Ya ce a yayin samamen, jami’an tsaro sun ƙwato babura da kuma bindigogi daga hannun waɗanda ake zargin.

Makama ya kuma yaba wa rundunar JTF bisa yadda suke sadaukar da rayuwarsu a kullum wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da kuma kare al’ummomi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *