Dilar kwaya ta mutu ana shari’arta a kotu

[ad_1]



Wata mata da ake zargi da dillancin miyagun kwayoyi ta mutu jim kadan bayan an gurfanar da ita a gaban kotu.

Dubun matar mai shekaru 52 ta cika ne bayan da fada hannun jami’an kwamitin aiki da cikawa na Jihar Edo a yayin da take sayar da kayan da ake zargin miyagun kwayoyi ne.

Daga bisani jami’an suka mika ta ga Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin gurfanarwa a gaban kotu.

Shaidu a kotun sun ce an ga alamar rashin koshin lafiya a tattare da matar a lokacin da jami’an hukumar suka kai ta kotu, lamarin da suka bayyana a matsayin rashin kulawa.

Wata majiya ta ce tun watan Janairu Hukumar NDLEA take tsare da matar take matar ba tare da an gurfanar da ita a kotu ba.

Dan marigayiyar, mai suna Samuel, ya bayyana cewa sun sha rokon hukumar ta gurfanar da ita a kotu. Ya ce, a ranar Litinin ya kamata a gurfanar da ita, amma ranar Talata ta yanke jiki a cikin kotu ta ce ga garinku nan.

Sai dai Kwamandan Hukumar NDLEA a Jihar Edo, Mitchell Ofoyeju, ya musanta zargin mutuwar wadda ake zargin yana da nasaba da sakaci daga bangaren jami’ansa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *