Taron APC: Kansilolin Kebbi Biyu Sun Mutu Da Wani Mashawarcin Gwamna A Abuja
[ad_1]
An tabbatar da mutuwar mutane uku yayin taron ƙasa na jam’iyyar APC da aka kammala kwanan nan a Abuja.
Mamatan sun haɗa da Hadiza Sabo Warrah, kansila mai wakiltar mazaɓar Warrah; da Sahabi Alheri, kansila mai wakiltar mazaɓar Birnin Yauri a ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi.
- Jirgi Marar Matuki Na Dakon Kaya Samfurin Changying-8 Ya Yi Nasarar Tashi A Karon Farko
- Amincewa Da Lamunin Dala Biliyan 6 cikin Sa’o’i 4: Atiku ya caccaki Tinubu da Majalisar Dattawa
Na ukunsu shi ne, Abubakar Sadiq, Babban Mataimaki na Musamman (SSA) ga gwamnan jihar Kebbi kan harkokin kafafen sada zumunta.
A cewar wata sanarwa da mai ba gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Yahaya Sarki, ya fitar, mutanen uku sun mutu ne yayin da wata mota ta buge su a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka titi. Lamarin ya faru ne bayan motarsu ta tsaya a kan hanya yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja domin halartar taron APC.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a cikin saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, ya bayyana cewa ya samu labarin rasuwarsu cikin matuƙar kaduwa, tare da roƙon Allah ya gafarta musu.
[ad_2]
Source link