Tinubu Ya Saita Wa Gwamna Yusuf Hanyar Sauya Sheƙa Zuwa APC
[ad_1]
Biyo bayan wata ganawar sirri da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano suka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, alamu sun nuna cewa; gwamnan na shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Wasu majiyoyi da ke da masaniya kan taron, sun shaida wa manema labarai cewa; tattaunawar ta warware matsalolin siyasa da tun farko suka kawo cikas ga yunƙurin sauya sheƙar da gwamnan ke shirin yi.
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a kan siyasar Kano, makwannin da suka gabata, inda rahotanni suka bayyana aniyar ta Yusuf na shiga jam’iyyar APC a matsayin wadda ta mamaye tarukan jama’a tare da dagula dangantakarsa da tsohon gwamna, kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, ƙoƙarin da Yusuf ya yi a ƴan makwannin nan, na da nasaba da rashin tabbas kan makomarsa ta siyasa a cikin jam’iyyar APC, musamman tabbacin da ya bayar game da sake tsayawa takara a 2027, da makomar tsarin siyasarsa a halin yanzu da kuma tsaron lafiyar magoya bayansa a cikin jam’iyyar mai mulki.
- Sin Ta Mika Sakon Ta’azziya Sakamakon Gobara Da Ta Kone Wani Babban Kanti A Pakistan
- Jita-jitar Sauya Sheƙa: Gwamna Yusuf Na Ganawar Sirri Da Tinubu A Aso Rock
Waɗancan batutuwa, in ji masu lura da al’amuran, an magance su ne a ganawar da suka yi da shugaba Tinubu.
Har ila yau, gwamna Yusuf ya ƙi yarda ya yi magana da manema labarai, bayan barinsa Villa, inda ya bayyana cewa, “zai sake dawowa.”
Rahotannin sun ce, an kwashe kusan sa’o’i uku ana ganawar. Domin kuwa, gwamnan ya isa fadar shugaban ƙasa ne tun misalin ƙarfe 4:10 na yamma, sanye da farar babban riga da jar hula, sannan ya bar fadar da bayan ƙarfe 7 na dare.
Tun a ƙarshen shekarar da ta gabata ne, ake ta faman cece-kuce kan batun sauya sheƙar ta Yusuf, biyo bayan dambarwar siyasar da ke nuni da sake daidaita alaƙarsa da gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Duk da cewa, gwamnan ya yi shiru a bainar jama’a a kan lamarin, amma wasu daga cikin muƙarrabansa da abokan siyasa a ƴan watannin nan, sun fito fili sun tattauna da shugabannin jam’iyyar APC a Kano da Abuja, lamarin da ya ƙara rura wutar tsammanin ɗaukar matakin da ya dace.
Sai dai, rahotanni a makon da ya gabata sun nuna cewa; shirin sauya sheƙar ya gamu da cikas bayan da aka ce shugabannin jam’iyyar APC, sun yi taka-tsan-tsan wajen bayar da ƙwaƙaran alƙawura, musamman kan batun tikitin sake komawa takarar gwamna kai tsaye a shekarar 2027.
Rahotanni sun nuna cewa, wannan jinkirin ya tilasta wa gwamnan yin tafiyar hawainiya, duk da cewa; wasu magoya bayansa a matakin ƙananan hukumomi da na unguwanni sun yi taro tare da nuna goyon bayan sauya sheƙar.
Ga dukkan alamu, ganawar ta ranar Litinin da shugaba Tinubu, ta sake farfaɗo da batun sayin sheƙar.
Majiyoyi sun ce, shugaban da kansa ya tabbatar wa Yusuf ƙimarsa ga lissafin siyasar APC, musamman a Kano da yankin Arewa maso Yamma, inda jam’iyyar ta sha kaye a zaben 2023.
[ad_2]
Source link