Gudunmawar Shehu Ibrahim Inyass (RTA) Ga Musulunci A Wayewar Zamani
[ad_1]
Waye Shehu Ibrahim Inyass wanda aka shirya taron Mulidin Katsina 2026 wanda aka rahoto sama da mutum miliyan Uku sun halarci taron na bana, kuma shi ne karo na 40 da ya yi daidai da cikar shekarunsa 126 a bana?
Mun gode Allah da ya kawo mu wannan lokaci na maulidin shehu Ibrahim radiyallahu ta’ala anhu (RTA), wanda za mu yi tarihinshi a taƙaice da gudunmawar da ya bai wa Musulunci, sannan kuma mu lissafo wasu daga cikin manyan almajiransa.
Shehu Ibrahim Inyass (RA) bawa ne na Allah wanda ya fifita lahirarsa akan duniyarsa, ya savawa san ransa a cikin abin da ubangijinsa yake so, ya hore kansa cikin ibadar Allah, da yaɗa Imani, da yaɗa ilimi a tsakiyar musulmai. Allah ya shiryar da shi mutanen da ba adadi, Allah ya shiryar dasu zuwa musulunci, waɗanda musulman ne kuma, Allah ya taimake shi akansu, ya ƙara musu imani, waɗanda mu’uminai ne kuma, Allah ya taimake shi akansu, ya kai su ga ihsani, albarkarsa. Da falalan Allah, ya zama miliyoyin mutane waɗanda da kafurai ne maguzawa, amma albarkar shehu Ibrahim (RA) sun Musulunta. A Nijeriya, ba a tava ganin ɗan ƙabilar Igbo ya musulunta ba sai a hannun Shehu Ibrahim Inyas (RA), kuma an samu rahotonnin irin hakan a wasu ƙasashe.
- Maulud 1,500: Yadda Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Ta Yi Maulidin Takutaha A Kaduna
- Shehu Mahy Inyass Ya Sanar Da Sauye-sauye A Tafiyar Tijjaniya A Nijeriya
Sannan, su kuma waɗanda Musulmai ne amma suka ƙara Imani suka zama cikin mu’uminai musamman a irin wannan zamani mai haɗari da ke cike da kimiyya da fasaha wanda in don ɗan karatu kaɗan da kake da shi wanda kake ganin babu wanda ya ke da ƙarfin yin wannan aiki sai Allah amma a yanzu za kaga mutum bawansa ya yi, toh kaga ai kana bukatar lalle a gyara karatu. Misali, Ubangiji ya faɗa cewa, babu wanda ya san abin ke cikin mahaifa, amma yanzu in matarka tana da juna-biyu, sai taje yin awon ciki, aka saka na’urar hasken wuta mai haska cikin jiki, sai ga shi an gano abin da ke cikin mahaifa, ana nufin Ƙur’ani ya faɗa ba daidai ba kenan, a’a, karatu ya tabbatar da cewa, ubangiji ya ce, ba wanda yasan abin da ke cikin mahaifa sai wanda aka sanar ma wa, Alhamdulillah tun da akwai waɗanda aka sanarwa, to an sanar.
Akwai, ire-iren waɗannan maganganu da yawa, kamar a fannin ruwan sama, babu wanda ya san yaushe ruwan sama zai sauka sai wanda ubangiji ya sanar da shi, ma’ana Ilimi wanda ga shi yanzu a fili. Malaman sanin yanayin sararin samaniya, Allah ya sanar da su, ranar da za a yi ruwa, a wuri kaza da wuri kaza, ban da wuri kaza da wuri kaza.
Wanda yake da ɗan ƙaramin ilimi duk sai ya gigice, amma a’a, Allah shi ya saukar da ilimi ya gaya mana waɗannan abubuwan duk da ilimi za’a san su, kuma ɗan adam kalifan Allah ne. Akan wannan abubuwan, Shehu Ibrahim Inyas, ya ƙara gyara mana imaninmu na fahimtar ubangijinmu da zamaninmu.
Shehu Ibrahim (RA) ya yi shekara 77 cikin ibada da karantarwa da musuluntarwa da imanantarwa da ihsanantarwa. Ya yi hajji, irin ta wancan lokaci, babu jirgin sama sai dai tafiyar kasa, jirgin ruwa da sauran ababen hawa, sannan kuma, ya yi hajji a zamanin jirgin sama, ya yi hajji kusan 17, Umrah kuma ba adadi, zuwa taro musamman na rabiɗa (majalisar kolin musulunci) a saudiyya da sauransu, duk ba adadi.
Shehu Ibrahim Inyass ya yaɗa musulunci a nan Afirka da Asiya, ya watsa jama’ansa – almajiransa a duniya, yau su suke ɗauke da tutar karantarwa da addinantarwa da ilimantarwa mai kyau mai tsafta a cikin wayewa da komai.
Yana da littattafai da yawa a mabanbantan vangarori na addini, da kuma mabanbantan ilimai. yana da babban littafin Diwani a tare waje guda kusan guda tara a cikin yabon manzon Allah SAW.
Ya shiga manyan ƙasashen duniya, kusan ƙasa ɗaya ce daga cikin manyan ƙasashe da Shehu Ibrahim bai shiga ba sabida wani dalili amma da ya bi gabas, sai da ya kai ƙarshenta, haka yamma, sai da ya kai ƙarshenta, har ya zama yana da muƙamai da yawa a cikin duniya duk da bai karvan muƙamai.
Don haka, ba za a yi mamaki ba in aka ce, shi ne ofishin haɗuwar jami’ar Azhar da jami’ar Kairawani ta magrib.
Shehu Ibrahim, shi ne mataimakin shugaban taron Musulunci da aka yi a Karaci a wuraren shakarar 1960. Yana daga cikin kwamitin kafa kungiyar rabiɗatul Alamil islami (Majalisar koli ta musulunci) amma akwai Takardu a hannu da ke nuna cewa, Shehu Ibrahim shi ya kafa kungiyar, ya kuma bayar da shawarwarin sharuɗɗa da ya kamata abi, wanda Alhamdulillah, har yau akan wannan sharuɗɗa kungiyar take amma sabida Shehu ba mutum ba ne mai zama wuri ɗaya, sai ya ɗora wani bawan Allah ɗan kasar Pakistan mai suna Sabbani a muƙaminsa har yau ‘ya’yansa, musamman khalifansa na yanzu, yana daga cikin kwamitin wannan babbar majalisar kolin harkokin musulunci ta saudiyya. Shehu Ibrahim shi ne ofishin haɗin kan jami’o’in kasashen musulunci, ya kafa wata kungiya ta jami’o’in kasashen musulunci a Rabat, Morocco.
Sannan yana daga cikin kwamatin sha’anin musulunci babba na Misra, “Majlisul A’ala lish’unil islamiya” na Misra, sannan yana daga cikin kwamiti babba na “kibarul ulama’I – manyan malamai na Misra”, wanda basu da yawa, duk shekara suke zama su kalli addini, su tattauna abubuwan da suka faru, mai ya dace a gyara da sauransu, yana daga cikin kwamitin “Majma’ul buhusil islamiya bil’ƙahira, sannan yana daga cikin kwamitin majalisar dattawa babba ta musulunci na kasar Jaza’ir, yana daga cikin manya-manyan kwamitin harkokin musulunci a duniya, yana da manya-manyan abubuwa, ya samu manya-manyan lambobin yabo na kasashen duniya, ciki har da nan Nijeriya tamu.
Ya kafa “Rabiɗatul alamul islami”, ya kafa kungiyar haɗin kan Afrika mai suna, “Ittihadul Ifriƙi” wanda ita ta zama kungiyar havaka tattalin arzikin ƙasashen yamma (ECOWAS), ya haɗa hannu da shugabannin Afrika, har sai da Afrika ta samu ‘yancin kai, duk kasar da ta samu ‘yancin kai zaka ga hannunsa a ciki, hatta tawagar Nijeriya masu zuwa amso ‘yancin kai, da suka je ‘Botos Gambia’ ya fito ya tarbe su, ya yi musu addu’a sannan ya yi izini. Bayan sun karvo, sai da suka kuma tsayawa a ‘Botos Gambia’.
Jaridun duniya, sun yi maganganun sa, an yi littafai akan sa, ya rubuta littattafai da dama, yana daga cikin abin da jaridun suka faɗa a lokacin rasuwarsa, ya rasu ya bar mutum miliyan talatin (30,000,000) dukkan su almajiransa ne, dukkan su suna binsa cikin abin da ya ɗora su.
To alhamdulillahi, muna yin Maulidin Shehu Ibrahim Inyas Kaulaka, sabida godiya da baiwar da Ubangiji ya yi mana na bamu kyautar shi (Shehu Ibrahim Inyas). Sabida shehu Ibrahim (RA), waliyyanmu na Afrika, malamanmu na Afrika, sun yi bushara da zuwansa, sun faɗi sunansa, sun faɗi sifarsa, sun faɗi jikinsa, sun faɗi garinsa, sun faɗi mahaifinsa. Shehu Ibrahim (RA) ba wani abu ne da aka tsince shi, ba a san da shi ba. Shehunmu, shehu Tijani (Abul Abbas), Morocco, ɗan Afirka ne, sai dai Balarabe ne, ya yi bushara faila zata zo a cikin almajiransa, wanda zai ɗaga wannan tsarin nasa na Imani, wanda shi ne jihadul akbar a faɗin Manzon Allah SAW, da cewa, “Yaƙi da makami, yaƙi ne ɗan ƙarami, amma ka yaƙi zuciyarka da son zuciyarka, shi ne yaƙi babba”. To yanzu wannan yaƙi ƙarami, wanda shi ne yaƙi da makami, karatunsa ake yi, akwai makarantun sojoji da ake koya dabarun yaƙi da sarrafa makamai, to haka shi ma yaƙi babba na zuciya, dole sai an shiga makarantar sufaye.
Makarantar sufanci, tafi mayar da hankali kan al’amuran zuciya, tun daga zuciya mai horo da lefi (Ammaratu bis-su’i), inda Ƙur’ani ke cewa, “wama ubarri’u nafsi, innan nafsa la’ammaratun bissu’I”, sai a yi karatu akanta, har a tashi daga kanta, a tafi zuciya mai zargin kanta (lawwama), inda Ƙur’ani ke cewa, “fala uƙsimu bin nafsil lawwama”, itama a yi karatu akanta, daga nan a tafi zuwa zuciyar da za ta iya gane gaskiya da ƙarya (Mulhamah), inda Ƙur’ani ke cewa,“wa nafsin wa ma sawwaha, fa’alhamaha fujuraha wa taƙwaha”, itace zuciyar da Allah yake kintsa mata abubuwa, har ka tashi daga nan kuma kazo zuciya mai tsarki (nafsuz zakiya), inda Ƙur’ani ke cewa, “ƙad aflaha man zakkaha wa ƙad kaba man dassaha”, har kuma ka tashi daga wannan ajin kazo zuciya Yardajjiya (Radiya) wadda ta yarda da hukuncin Allah, ta sallama wa Allah hukuncin sa, ba fushi ba damuwa ba kaza, har kazo kuma zuciya (mardiya) wadda ita ma Allah ya yarda da ita, har kazo zuciya (mutuma’inna) wadda ta ɗinasu, har kazo zuciya (Arifa), zuciya mai (Muraƙaba), har kazo zuciya mai (Mushahada), wannan ita ce makarantar sufaye.
Yadda kaga wannan ilimi da ake yi na wannan makarantar sojoji na zahiri, wannan yaki na zahiri na tsaron kasa, to haka kuma wannan yaki babba na baɗini, ba haka kawai mutum zai ce zan iya shiryar da kaina ba, a’a ƙarya ne, tunda ba haka kawai mutum zai ce, zan ɗau makami, zan iya sarrafa shi, sai ace ɗan fashi ne, a kama shi.
[ad_2]
Source link